2 Sam 18:4-21 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. Sai sarki ya ce musu, “Duk abin da kuka ga ya fi muku kyau, shi zan yi.” Sarki kuwa ya tsaya a bakin ƙofar garin sa'ad da sojojin suke fita, kashi kashi, ɗari ɗari, da dubu dubu.

5. Ya kuma umarci Yowab, da Abishai, da Ittayi ya ce, “Ku lurar mini da saurayin nan, Absalom.” Dukan sojojin suka ji umarnin da sarki ya yi wa shugabanninsu a kan Absalom.

6. Sojojin suka tafi zuwa karkara don su yi yaƙi da mutanen Isra'ila. Suka yi yaƙin a kurmin Ifraimu.

7. Mutanen Isra'ila suka sha kashi a hannun jarumawan Dawuda. A wannan rana aka kashe mutane da yawa, har mutum dubu ashirin (20,000).

8. Yaƙin ya bazu ko'ina a ƙasar. A ranar abin da kurmin ya ci ya fi abin da aka kashe da takobi.

9. Absalom yana cikin gudu sai ya fāɗa a hannun jarumawan Dawuda. Sa'ad da yake cikin gudu a kan alfadarinsa, sai alfadarin ya kurɗa tsakanin rassan babban itacen oak. Kansa ya sarƙafe kam cikin rassan itacen oak ɗin, alfadarin kuwa ya wuce, ya bar shi yana rataye yana lilo.

10. Da wani mutum ya gani, sai ya tafi ya faɗa wa Yowab, ya ce, “Na ga Absalom yana reto a itacen oak.”

11. Yowab ya ce wa mutumin da ya faɗa masa, “Kai! Ka gan shi! Me ya sa ba ka buge shi har ƙasa ba? Ai, da na ba ka azurfa goma da abin ɗamara.”

12. Sai mutumin ya ce wa Yowab, “Ko da za a ba ni azurfa dubu a hannuna, ba zan miƙa hannuna in taɓa ɗan sarki ba, gama a kunnuwanmu sarki ya umarce ka, kai da Abishai, da Ittayi cewa, ‘Ku lura mini da saurayin nan, Absalom.’

13. In da na ci amana har na kashe shi, ba yadda abin zai ɓoyu ga sarki, sa'an nan kai da kanka ka zame, ka bar ni.”

14. Yowab ya ce, “Ba zan ɓata lokaci haka da kai ba.” Sai ya ɗibi mashi uku ya soki Absalom a ƙahon zuciya, tun yana da sauran rai, a maƙale cikin itacen oak.

15. Sa'an nan samari goma masu ɗaukar wa Yowab makamai, suka kewaye Absalom, suka yi ta dūkansa har ya mutu.

16. Sa'an nan Yowab ya busa ƙaho, sojoji suka komo daga runtumar Isra'ilawa. Yowab ya tsai da su.

17. Suka ɗauki gawar Absalom, suka jefa ta cikin wani rami mai zurfi a kurmin, suka tula tsibin duwatsu a kanta. Dukan Isra'ilawa kowa ya tsere zuwa gidansa.

18. Tun Absalom yana da rai ya gina wa kansa al'amudi a kwarin sarki, gama ya ce, “Ba ni da ɗa wanda zai sa a riƙa tunawa da ni.” Ya kira al'amudin da sunansa. Ana kuwa kiransa al'amudin Absalom har wa yau.

19. Ahimawaz ɗan Zadok ya ce wa Yowab, “Ka yarda mini in sheƙa a guje in kai wa sarki labari yadda Ubangiji ya cece shi daga hannun magabtansa.”

20. Yowab ya ce masa, “Ba za ka kai labari yau ba, sai wata rana ka kai, amma yau ba za ka kai labari ba, domin ɗan sarki ya mutu.”

21. Sa'an nan Yowab ya ce wa wani mutumin Habasha, “Tafi ka faɗa wa sarki abin da ka gani.” Sai Bahabashen ya rusuna wa Yowab, sa'an nan ya sheƙa a guje.

2 Sam 18