2 Sam 18:9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

Absalom yana cikin gudu sai ya fāɗa a hannun jarumawan Dawuda. Sa'ad da yake cikin gudu a kan alfadarinsa, sai alfadarin ya kurɗa tsakanin rassan babban itacen oak. Kansa ya sarƙafe kam cikin rassan itacen oak ɗin, alfadarin kuwa ya wuce, ya bar shi yana rataye yana lilo.

2 Sam 18

2 Sam 18:5-13