L. Kid 18:2-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

2. Ka kawo 'yan'uwanka tare da kai, wato kabilar Lawi, kakanka, don su yi muku aiki sa'ad da kai da 'ya'yanka kuke gaban alfarwa ta sujada.

3. Za su taimake ku, su kuma yi dukan ayyukan alfarwa. Amma fa, ba za su kusaci kayayyakin Wuri Mai Tsarki, ko bagade ba, don kada su, har da ku, ku mutu.

4. Za su haɗa kai da ku su lura da alfarwa ta sujada da dukan aikace-aikace na cikin alfarwar. Kada wani dabam ya kusace ku.

5. Ku lura da ayyukan Wuri Mai Tsarki da na bagade don kada hasala ta sāke fāɗa wa Isra'ilawa.

6. Ga shi, ni na ɗauki 'yan'uwanku, Lawiyawa, daga cikin mutanen Isra'ila. Kyauta suke a gare ku, waɗanda aka bayar ga Ubangiji don su lura da alfarwa ta sujada.

7. Da kai, da 'ya'yanka za ku yi aikin firist da duk abin da ya shafi bagade da aiki na bayan labule. Ku ne za ku yi wannan aiki. Na ba ku aikin firist ya zama naku. Duk wani dabam wanda ya zo kuwa, za a kashe shi.”

8. Ubangiji ya kuma ce wa Haruna, “Na ba ka aikin lura da hadayuna na ɗagawa, wato sadakokin Isra'ilawa, na ba ka su su zama rabonka da na 'ya'yanka har abada.

9. Abin da ya ragu daga cikin hadaya mafi tsarki da ake miƙa mini zai zama rabonka da na 'ya'yanka, wato daga kowace hadaya, da hadaya ta gari, da hadaya don zunubi, da hadaya don laifi.

10. A wuri mai tsarki za ku ci shi, kowane namiji ya iya ci. Abu mai tsarki ne a gare ka.

11. “Har yanzu kuma duk sadakokin da Isra'ilawa suke bayarwa don hadaya ta ɗagawa da ta kaɗawa, na ba ka, kai da 'ya'yanka mata da maza, a kowane lokaci. Duk wanda yake da tsarki a gidanka zai iya ci.

12. “Duk mai mafi kyau, da ruwan inabi mafi kyau duka, da hatsi mafi kyau duka na nunan fari, waɗanda suke bayarwa ga Ubangiji, na ba ku.

13. Nunan fari na dukan amfanin gonarsu wanda suke kawowa ga Ubangiji, zai zama naka. Duk wanda yake da tsarki a gidanka zai iya cinsa.

14. “Iyakar abin da aka keɓe wa Ubangiji a Isra'ila zai zama naka.

15. “Dukan haihuwar fari, ko ta mutum ko ta dabba da sukan bayar ga Ubangiji zai zama naka. Amma ka fanshi kowace haihuwar fari ta mutum, ko ta dabbar da take haram.

L. Kid 18