4. Sai ya ce masa, “Ya ɗan sarki, me ya sa kake damuwa kowace rana? Ba za ka faɗa mini ba?”Sai Amnon ya ce masa, “Na jarabtu ne da Tamar ƙanwar ɗan'uwana Absalom.”
5. Yonadab kuwa ya ce masa, “Kwanta a gadonka ka yi kamar kana ciwo, lokacin da mahaifinka ya zo domin ya duba ka, sai ka ce masa, ‘A bar ƙanwata Tamar ta zo ta ba ni abinci, ta riƙa shirya abincin a idona, don in gani in kuma riƙa ci daga hannunta.’ ”
6. Amnon kuwa ya kwanta, ya yi kamar yana ciwo.Sa'ad da sarki ya zo duba shi, sai Amnon ya ce wa sarki, “Ina roƙo a sa ƙanwata, Tamar, ta zo ta toya mini waina a inda nake, ta riƙa ba ni da hannunta ina ci.”
7. Sai Dawuda ya aika gida, wurin Tamar, ya ce, “Tafi gidan Amnon wanki, ki shirya masa abinci.”
8. Tamar kuwa ta tafi gidan wanta Amnon, inda yake kwance. Sai ta ɗauki ƙullu, ta cuɗa, ta toya waina a idonsa.
9. Ta juye wainar daga kaskon yana gani, amma ya ƙi ci. Ya ce wa waɗanda suke cikin ɗakin su fita. Su kuwa suka fita.
10. Sa'an nan Amnon ya ce wa Tamar, “Kawo abincin a cikin ɗakin kwanana, ki riƙe mini in ci.” Sai ta ɗauki wainar da ta yi, ta kai wa Amnon, wanta, a ɗakin kwana.
11. Amma da ta kawo kusa da shi don ya ci, ya kama ta, ya ce, “Zo in kwana da ke ƙanwata.”
12. Ta ce masa, “Haba, wana, kada ka ƙasƙantar da ni, gama ba a yin haka a cikin Isra'ila, kada ka yi halin dabba.
13. Ni kuwa ina zan sa kaina saboda kunya? Kai kuwa za ka zama ɗaya daga cikin riƙaƙƙun sakarkarin mutane na cikin Isra'ila. Ina roƙonka ka yi magana da sarki, gama ba zai hana ka ka aure ni ba.”
14. Amma Amnon bai ji maganarta ba. Da yake ya fi ta ƙarfi, sai ya yi mata faɗe.
15. Bayan haka sai Amnon ya ƙi ta da mummunar ƙiyayya, har ƙiyayyar ta fi yawan ƙaunar da ya yi mata. Ya ce mata, “Tashi, ki fita.”
16. Sai ta ce masa, “A'a wana, muguntar koran nan da kake yi mini, ta fi ta wadda ka riga ka yi mini.”Amma bai kasa kunne gare ta ba.
17. Sai ya kira baran da yake yi masa hidima, ya ce, “Fitar da matan nan daga gabana, ka rufe ƙofa.”
18. Tamar kuwa tana saye da doguwar riga mai hannuwa, gama haka gimbiyoyi budurwai suke ado. Baran Amnon kuwa ya fitar da ita, ya kulle ƙofar.
19. Tamar ta baɗe kanta da toka, ta keta doguwar rigarta mai hannuwa wadda ta sa, ta rufe fuska da hannu, ta tafi tana ta kuka da ƙarfi.
20. Absalom wanta ya tambaye ta, ya ce, “Ko Amnon wanki ya ɓata ki? To, yi shiru, ƙanwata, shi wanki ne, kada ki damu da yawa.” Tamar kuwa ta zauna a kaɗaice a gidan Absalom wanta.
21. Da Dawuda sarki ya ji wannan, sai ya husata ƙwarai.