1. A kwanakin nan Filistiyawa suka tattara sojojinsu don su yi yaƙi da Isra'ilawa. Akish kuwa ya ce wa Dawuda, “Sai ka sani fa, kai da mutanenka za ku tafi tare da ni da sojojina.”
2. Sai Dawuda ya ce, “Za ka ga abin da baranka zai yi.”Akish ya ce wa Dawuda, “Da kyau, zan sa ka cikin zaunannun jarumawan da suke kāre ni.”
3. Sama'ila ya riga ya rasu, dukan Isra'ilawa kuwa suka yi makoki dominsa, suka binne shi a garinsu, wato Rama. Saul kuma ya riga ya kori masu duba da masu maita daga ƙasar.
4. Filistiyawa suka kafa sansaninsu a Shunem. Saul ya tattara Isra'ilawa, su ma suka kafa sansaninsu a Gilbowa.
5. Da Saul ya ga rundunar yaƙin Filistiyawa, sai ya tsorata, ya yi rawar jiki ƙwarai.
6. Saul kuwa ya yi tambaya ga Ubangiji, Ubangiji bai amsa masa ba, ko ta mafarkai, ko ta Urim, ko ta annabawa.
7. Sai ya ce wa barorinsa, “Ku nemo mini wata mace mai duba domin in tafi wurinta in yi tambaya.”Barorinsa suka ce masa, “Ai, akwai wata mai duba a Endor.”
8. Sai Saul ya ɓad da kama, ya sa waɗansu tufafi. Shi da waɗansu mutum biyu suka tafi wurin matar da dare. Ya ce mata, “Ina roƙonki ki duba mini ta hanyar sihiri. Ki hawar mini da duk wanda zan faɗa miki.”
9. Matar ta ce masa, “Hakika ka san abin da sarki Saul ya yi, yadda ya karkashe masu duba da masu maita a ƙasar. Me ya sa kake ƙoƙarin kafa mini tarko, don ka sa a kashe ni?”
10. Saul ya rantse mata da Ubangiji, ya ce, “Hakika, ba za a hukunta ki saboda wannan ba.”
11. Sai matar ta ce, “Wa kake so in hawar maka?”Ya ce, “Ki hawar mini da Sama'ila.”
12. Da matar ta ga Sama'ila, sai ta fasa ƙara, ta ce wa Saul, “Don me ka ruɗe ni, ashe, kai ne sarki Saul?”
13. Sarki kuwa ya ce mata, “Kada ki ji tsoro, me kike gani?”Ta ce masa, “Na ga wani allah yana fitowa daga ƙasa.”
14. Ya ce mata, “Yaya kamanninsa yake?”Ta ce, “Wani tsoho ne yake hawowa, yana naɗe da alkyabba.”Saul ya gane Sama'ila ne, sai ya sunkuyar da kai, ya durƙusa har ƙasa da bangirma.
15. Sai Sama'ila ya ce wa Saul, “Don me ka dame ni, ka hawar da ni?”Saul ya ce, “Ina cikin babbar wahala, gama Filistiyawa suna yaƙi da ni, Allah kuma ya rabu da ni, ya ƙi amsa mini ko ta wurin annabawa ko ta mafarkai, saboda haka na kira ka, ka faɗa mini abin da zan yi.”
16. Sai Sama'ila ya ce masa, “Don me za ka tambaye ni, tun da yake Ubangiji ya rabu da kai, ya zama magabcinka?