9. Kusa da su kuma sai Refaya ɗan Hur, mai mulkin rabin yankin Urushalima, ya yi gyare-gyare.
10. Kusa da Refaya kuma, sai Yedaiya ɗan Harumaf ya yi gyare-gyare daura da gidansa.Kusa da Yedaiya sai Hattush ɗan Hashabnaiya ya yi gyare-gyare.
11. Malkiya ɗan Harim, da Hasshub ɗan Fahat-mowab suka gyara wani sashi da kuma Hasumiyar Tanderu.
12. Kusa da su kuma, sai Shallum ɗan Hallohesh mai mulkin rabin yankin Urushalima ya yi gyare-gyare tare da 'ya'yansa mata.
13. Hanun da mazaunan Zanowa suka gyara Ƙofar Kwari. Sun gina ta, suka sa ƙyamarenta, da sandunan ƙarfe na kulle ƙofofinta, da ƙyamarenta, suka gyara garun kamu dubu, har zuwa Ƙofar Juji.
14. Malkiya ɗan Rekab, mai mulkin yankin Bet-akkerem, ya gyara Ƙofar Juji. Ya gina ta, ya sa ƙyamarenta da sandunan ƙarfe na kulle ƙofofinta.
15. Sai Shallum ɗan Kolhoze, mai mulkin yankin Mizfa ya gyara Ƙofar Maɓuɓɓuga, ya gina ta, ya rufe ta, ya sa ƙyamarenta, da sandunan ƙarfe na kulle ƙofofinta. Ya kuma gina garun Tafkin Siluwam na gonar sarki, har zuwa matakan da suka gangaro daga Birnin Dawuda.
16. Bayansa kuma Nehemiya, ɗan Azbuk, mai mulkin yankin Bet-zur ya yi gyare-gyare, har zuwa wani wuri daura da kabarin Dawuda, har zuwa haƙaƙƙen tafki da gidan masu tsaro.
17. Waɗannan Lawiyawa sun yi gyare-gyare a ƙarƙashin shugabancin Rehum ɗan Bani.Kusa da su kuma, sai Hashabiya mai mulkin rabin yankin Kaila, ya yi gyare-gyare domin yankinsa.
18. Bayansa kuma, sai 'yan'uwansu suka yi gyare-gyare a ƙarƙashin shugabancin Bawwai ɗan Henadad, mai mulkin rabin yankin Kaila.
19. Kusa da su kuma sai Ezer ɗan Yeshuwa, mai mulkin Mizfa, ya gyara wani sashi a gaban gidan makamai a wajen kusurwa.
20. Bayansa kuma, Baruk ɗan Zabbai, ya gyara wani sashi daga wajen kusurwar, har ya zuwa ƙofar gidan Eliyashib babban firist.
21. Bayansa kuma Meremot ɗan Uriya, ɗan Hakkoz, ya gyara wani sashi daga ƙofar gidan Eliyashib, zuwa ƙarshen gidan.
22. Bayansa kuma sai firistoci, mutanen filin kwari, suka yi gyare-gyare.
23. Bayansu kuma Biliyaminu da Hasshub suka yi gyara daura da gidansu. Bayansu kuma Azariya, ɗan Ma'aseya, wato jikan Ananiya, ya yi gyara kusa da gidansa.