Waɗannan Lawiyawa sun yi gyare-gyare a ƙarƙashin shugabancin Rehum ɗan Bani.Kusa da su kuma, sai Hashabiya mai mulkin rabin yankin Kaila, ya yi gyare-gyare domin yankinsa.