Neh 12:26-38 Littafi Mai Tsarki (HAU)

26. Waɗannan suna nan a zamanin Yoyakim ɗan Yeshuwa, jikan Yehozadak, da zamanin mai mulki Nehemiya, da Ezra, firist da magatakarda.

27. A lokacin keɓe garun Urushalima, sai aka nemo Lawiyawa a wurarensu duka don a kawo su Urushalima, su yi bikin keɓewa da farin ciki da godiya, da raira waƙoƙi da kuge, da garaya, da molo.

28. Aka tattara mawaƙa daga kewayen Urushalima da ƙauyukan Netofatiyawa.

29. Da kuma daga Betgilgal da karkarar Geba, da Azmawet, gama mawaƙan sun gina wa kansu ƙauyuka kewaye da Urushalima.

30. Sai firistoci da Lawiyawa suka tsarkake kansu, suka kuma tsarkake jama'a, da ƙofofi, da garun.

31. Sai na sa shugabannin Yahuza su hawo garu, sa'an nan na sa manyan ƙungiyoyi biyu waɗanda za su yi godiya, su tafi a jere.Ƙungiya guda ta bi wajen dama a kan garun zuwa Ƙofar Juji.

32. Hoshaiya da rabin sugabannin Yahuza suka bi bayansu,

33. tare da Azariya, da Ezra, da Meshullam,

34. da Yahuza, da Biliyaminu, da Shemaiya, da Irmiya.

35. Sa'an nan waɗansu 'ya'yan firistoci, masu busar ƙaho, su ne Zakariya ɗan Jonatan, jīkan Shemaiya. Sauran kakanninsa su ne Mattaniya, da Mikaiya, da Zakkur, daga zuriyar Asaf.

36. Sauran 'yan'uwansa su ne Shemaiya, da Azarel, da Milalai, da Gilalai, da Ma'ai, da Netanel, da Yahuza, da Hanani. Suna da kayayyakin bushe-bushe da na kaɗekaɗe. Ezra magatakarda ne yake gabansu.

37. A Ƙofar Maɓuɓɓuga kuwa, sai suka yi gaba sosai wajen matakan birnin Dawuda, wajen hawan garu, daga bisa gidan Dawuda, zuwa Ƙofar Ruwa wajen gabas.

38. Ƙungiyar jama'a ta biyu ta masu yin waƙoƙin godiya, ta bi ta wajen hagu. Na bi su tare da rabin jama'a a kan garu, sama da Hasumiyar Tanderu zuwa garu mai fādi,

Neh 12