2 Sar 10:6-24 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. Sa'an nan Yehu ya rubuta musu wasiƙa ta biyu, ya ce, “Idan kuna goyon bayana, idan kuma kun shirya za ku yi mini biyayya, to, sai ku fille kawunan 'ya'yan Ahab, sa'an nan ku zo wurina a Yezreyel gobe war haka.”'Ya'yan sarki, maza, su saba'in ne, suna a hannun manyan mutanen birni ne waɗanda suke lura da su.

7. Da wasiƙar ta iso wurinsu, sai suka kwashi 'ya'yan sarki guda saba'in, suka karkashe su. Suka sa kawunansu cikin kwanduna, suka aika wa Yehu a Yezreyel.

8. Da aka faɗa masa cewa an kawo kawunan 'ya'yan sarki, sai ya ce, “Ku ajiye su kashi biyu a ƙofar garin har safiya.”

9. Da safe, sa'ad da ya fita, ya tsaya, sai ya ce wa mutane duka, “Ba ku da laifi, ni ne na tayar wa maigidana har na kashe shi, amma wane ne ya kashe dukan waɗannan?

10. Ku sani fa ba maganar da Ubangiji ya faɗa a kan gidan Ahab da ba za ta cika ba, gama Ubangiji ya aikata abin da ya faɗa ta bakin bawansa Iliya.”

11. Haka kuwa Yehu ya karkashe waɗanda suka ragu na gidan Ahab a Yezreyel, wato dukan manyan mutanensa, da abokansa, da firistocinsa. Bai rage masa ko guda ba.

12. Yehu kuma ya fita zai tafi Samariya. A hanya, sa'ad da yake a Bet-eked ta makiyaya,

13. sai ya sadu da 'yan'uwan Ahaziya Sarkin Yahuza, sai ya ce, “Ku su wane ne?”Sai suka amsa, “Mu 'yan'uwan Ahaziya ne, mun zo mu gai da 'ya'yan sarki ne da 'ya'yan sarauniya.”

14. Yehu kuwa ya ce, “Ku kama su da rai.” Sai suka kama su da rai, suka karkashe su a ramin Bet-eked, su arba'in da biyu ne, ba a rage ko ɗaya a cikinsu ba.

15. Da ya tashi daga can, sai ya sadu da Yehonadab ɗan Rekab yana zuwa ya tarye shi. Yehu ya gaishe shi, ya tambaye shi, “Zuciyarka ta amince da ni kamar yadda tawa ta amince da kai?”Yehonadab ya amsa, “I.”Sai Yehu ya ce, “Idan haka ne, to, miƙo mini hannunka.” Sai ya miƙa masa hannunsa. Yehu kuwa ya ɗauke shi zuwa cikin karusa.

16. Ya ce, “Ka zo tare da ni, ka ga kishin da nake da shi domin Ubangiji.” Sai suka tafi cikin karusarsa.

17. Da suka isa Samariya, sai ya kashe duk wanda ya ragu na gidan Ahab a Samariya. Ya share mutanen gidan Ahab kaf kamar yadda Ubangiji ya faɗa ta bakin annabi Iliya.

18. Yehu kuwa ya tara mutane duka, ya ce musu, “Ahab ya bauta wa Ba'al kaɗan, amma Yehu zai bauta masa da yawa.

19. Saboda haka, yanzu sai ku kirawo mini dukan annabawan Ba'al, da dukan masu yi masa sujada, da dukan firistocinsa. Kada a manta da wani, gama ina da babbar hadayar da zan miƙa wa Ba'al. Duk wanda bai zo ba, za a kashe shi.” Amma dabara ce Yehu yake yi don ya hallaka waɗanda suke yi wa Ba'al sujada.

20. Yehu kuma ya sa a yi muhimmin taro saboda Ba'al. Aka kuwa kira taron,

21. sai ya aika cikin Isra'ila duka, dukan masu yi wa Ba'al sujada kuwa suka zo, ba wanda bai zo ba. Suka shiga, suka cika haikalin Ba'al makil daga wannan gefe zuwa wancan.

22. Sa'an nan Yehu ya ce wa wanda yake lura da ɗakin tufafi, “Ku fito da tufafi na dukan waɗanda suke yi wa Ba'al sujada.” Shi kuwa ya fito musu da tufafin.

23. Bayan wannan Yehu ya shiga haikalin Ba'al tare da Yehonadab ɗan Rekab, ya ce wa masu yi wa Ba'al sujada, “Ku bincike, ku tabbata, ba wani bawan Ubangiji tare da ku, sai dai masu yi wa Ba'al sujada kaɗai.”

24. Sa'an nan Yehu da Yehonadab suka shiga don su miƙa sadaka da hadayu na ƙonawa. Yehu ya riga ya sa mutum tamanin a waje, ya ce musu, “Mutumin da ya bar wani daga cikin waɗanda na bashe su a hannunku ya tsere, to, a bakin ransa.”

2 Sar 10