1. Sarki Sulemanu shi ne sarkin dukan Isra'ila,
2-6. waɗannan kuma su ne manyan fādawansa,Azariya ɗan Zadok shi ne firist.Elihoref da Ahija 'ya'yan Seraiya,maza, su ne magatakarda.Yehoshafat ɗan Ahilud shi ne mailura da takardu.Benaiya ɗan Yehoyada shi neshugaban sojoji.Zadok da Abiyata su ne firistoci.Azariya ɗan Natan shi ne shugabanhakimai.Zabud ɗan Natan shi ne mashawarcinsarki da abokinsa.Ahishar shi ne mai lura da bayin fāda.Adoniram ɗan Abda, shi ne mai lurada aikin gandu.
7. Sulemanu kuma ya naɗa mutum goma sha biyu a lardunan Isra'ila. Su ne za su tanaji abinci daga lardunansu domin sarki da iyalinsa. Kowane hakimi yakan kawo abinci wata guda a shekara.
20. Mutanen Yahuza da na Isra'ila suka yi yawa kamar yashi a bakin teku. Suka ci, suka sha, suka yi murna.
21. Sulemanu ya sarauci dukan mulkoki tun daga Kogin Yufiretis a gabas, har zuwa ƙasar Filistiyawa a yamma, daga kudu kuma har zuwa iyakar Masar. Su kuwa suka yi ta kawo wa Sulemanu harajinsu, ya kuwa mallake su dukan kwanakin ransa.
22. Abincin gidan Sulemanu na rana ɗaya garwa talatin na lallausan gari ne, da garwa sittin na gari,
23. da turkakkun bijimai goma, da shanu ashirin daga makiyaya, da tumaki ɗari banda kishimai, da bareyi, da batsiyoyi, da kaji masu ƙiba.
24. Sulemanu ya mallaki dukan ƙasar da yake yamma da Kogin Yufiretis, daga Tifsa har zuwa birnin Gaza. Ya mallaki dukan sarakuna yammacin Yufiretis. Akwai zaman lafiya ko'ina a mulkinsa da ƙasashen maƙwabta.
25. Mutanen Yahuza da na Isra'ila suka zauna lafiya tun daga Dan har Biyersheba. Kowa ya yi zamansa a gida dukan kwanakin Sulemanu.
26. Sulemanu kuma yana da rumfuna dubu arba'in (40,000) domin dawakan karusansa, da mahayan dawakai dubu goma sha biyu (12,000).
27. Hakiman nan nasa sha biyu, kowa ya kawo wa Sulemanu abinci, duk da waɗanda suke zuwa teburin cin abincin Sulemanu. Kowane hakimi yakan kawo abincin da za a ci na wata guda. Ba su fasa kawowa ba.
28. Suka kuma kawo sha'ir da ingirci domin dawakan da suke jan karusai, da sauran dabbobin da suke aiki. Kowanne bisa ga abin da aka sa masa.