1 Sam 9:1-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Akwai wani mutum daga kabilar Biliyaminu, sunansa Kish, ɗan Abiyel, jikan Zeror, na iyalin Bekorat, dangin Afinya, shi attajiri ne.

2. Yana da wani ɗa, sunansa Saul, kyakkyawan saurayi ne. A cikin jama'ar Isra'ila ba wanda ya fi shi kyau, ya fi kowa tsayi a cikin Isra'ilawa duka.

3. Ana nan sai jakunan Kish, mahaifin Saul suka ɓace, Kish kuwa ya ce wa Saul, ɗansa, “Tashi, kai da ɗaya daga cikin barorin ku tafi, ku nemo jakunan.”

4. Suka bi ta ƙasar tudu ta Ifraimu, suka ratsa ta ƙasar Shalisha, amma ba su same su ba. Suka kuma bi ta ƙasar Shalim, a can ma ba su same su ba. Sai suka bi ta ƙasar Biliyaminu, amma ba su same su ba.

5. Da suka kai ƙasar Zuf, sai Saul ya ce wa baransa da yake tare da shi, “Zo mu koma gida, kada babana ya bar damuwa a kan jakunan ya yi ta damuwa a kanmu.”

6. Amma baran ya ce masa, “Ai, akwai wani mutumin Allah a garin nan, ana kuwa ganin girmansa, domin duk abin da ya faɗa yakan zama gaskiya. Mu tafi can wurinsa, watakila ya iya faɗa mana inda jakunanmu suke.”

7. Saul ya ce wa baransa, “Idan muka tafi, me za mu ba shi? Gama guzurin da yake tare da mu ya ƙare, ba mu da wani abin da za mu ba shi.”

8. Baran kuma ya ce wa Saul, “Ina da 'yar azurfa tsaba da zan ba shi domin ya faɗa mana inda za mu same su.”

9. (A dā a Isra'ila, idan wani yana so ya yi tambaya ga Allah, sai ya ce, “Zo, mu tafi wurin maigani.” Gama wanda ake ce da shi annabi yanzu, a dā akan ce da shi maigani.)

10. Sai Saul ya ce wa baransa, “Maganarka daidai ce, zo, mu tafi.” Suka kuwa tafi garin da mutumin Allah yake.

1 Sam 9