Zak 10:2-6 Littafi Mai Tsarki (HAU)

2. Gama maganar shirme kan gida yake yi,Masu dūba suna ganin wahayin ƙarya,Masu mafarkai suna faɗar ƙarya,Ta'aziyyarsu ta banza ce.Domin haka mutane suna ta yawo kamar tumaki,Suna shan wahala saboda rashin makiyayi.

3. Ubangiji ya ce,“Ina fushi ƙwarai da makiyayan,Zan kuwa hukunta shugabannin,Gama ni Ubangiji Mai Runduna zan lura da garkena,Wato jama'ar Yahuza.Zan mai da su dawakaina na yaƙi.

4. Daga cikinsu za a sami mafificin dutsen gini,Daga cikinsu kuma za a sami turken alfarwa,Daga cikinsu za a sami bakan yaƙi,Daga cikinsu kuma kowane mai mulki zai fito.

5. Za su zama kamar ƙarfafan mutane cikin yaƙi,Za su tattaka maƙiyi a cikin taɓon tituna.Za su yi yaƙi, gama Ubangiji yana tare da su,Za su kunyatar da sojojin doki.

6. “Zan sa jama'ar Yahuza ta yi ƙarfi,Zan ceci jama'ar Yusufu.Zan dawo da su domin ina jin tausayinsu.Za su zama kamar waɗanda ban taɓa ƙyale su ba,Gama ni Ubangiji Allahnsu ne,Zan amsa musu.

Zak 10