Zak 1:9-21 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Sai na ce, “Mene ne waɗannan, ya Ubangiji?”Mala'ikan da ya yi magana da ni ya ce, “Zan bayyana maka ma'anarsu.”

10. Sai mutumin da yake tsaye a cikin itatuwan ci-zaƙin ya amsa ya ce, “Waɗannan su ne Ubangiji ya aike su su yi tsaron duniya, suna kai da kawowa.”

11. Sai suka ce wa mala'ikan Ubangiji wanda yake tsaye a cikin itatuwan ci-zaƙin, “Mun yi ta kai da kawowa a duniya, sai muka ga duniya duka tana zaman lafiya.”

12. Sa'an nan mala'ikan Ubangiji ya ce, “Ya Ubangiji Mai Runduna, har yaushe za ka ƙi nuna jinƙai ga Urushalima da biranen Yahuza, waɗanda kake jin haushinsu shekara saba'in ke nan?”

13. Sai Ubangiji ya amsa wa mala'ikan da yake magana da ni da magana ta alheri da ta ta'azantarwa.

14. Mala'ikan kuma da yake magana da ni ya ce, in yi shela in ce, “Ubangiji Mai Runduna ya ce yana jin ƙishin Urushalima da Sihiyona ƙwarai.

15. Yana fushi ƙwarai da al'umman duniya da take zaman lafiya, gama ya yi ɗan fushi da mutanena, amma su suka yi musu hukuncin da ya zarce.

16. Saboda haka shi Ubangiji zai koma ya ji juyayin Urushalima. Za a gina Haikalinsa a cikinta, zai kuma auna Urushalima da ma'auni.”

17. Ya ce, in kuma yi shela, in ce, “Ubangiji Mai Runduna ya ce wadata za ta sake bunƙasa cikin biranensa, zai kuma ta'azantar da Sihiyona, ya kuma zaɓi Urushalima.”

18. Da na ɗaga idona, sai na ga ƙahoni huɗu.

19. Sai na ce wa mala'ikan da ya yi magana da ni, “Mene ne waɗannan?”Shi kuwa ya ce mini, “Waɗannan su ne ƙahonin da suka warwatsa Yahuza, da Isra'ila, da Urushalima.”

20. Sa'an nan kuma Ubangiji ya nuna mini waɗansu maƙera, su huɗu.

21. Sai na ce, “Me waɗannan suke zuwa su yi?”Sai ya ce, “Waɗannan su ne ƙahonin da suka warwatsa Yahuza don kada mutum ya ɗaga kansa. Waɗannan kuwa sun zo don su tsorata su, su karya ƙahonin al'umman duniya waɗanda suka ɗaga ƙahoninsu gāba da ƙasar Yahuza don su warwatsa ta.”

Zak 1