Yah 13:19-37 Littafi Mai Tsarki (HAU)

19. Tun yanzu zan sanar da ku abu tun bai faru ba, domin sa'ad da ya faru ku ba da gaskiya ni ne shi.

20. Lalle hakika, ina gaya muku, wanda ya yi na'am da duk wanda na aiko, ya yi na'am da ni ke nan. Wanda ya yi na'am da ni kuwa, to, ya yi na'am da wanda ya aiko ni.”

21. Bayan da Yesu ya faɗi haka, ya ji nauyi a ransa, ya yi shaida ya ce, “Lalle hakika, ina gaya muku, ɗayanku zai bāshe ni.”

22. Sai almajiran suka duddubi juna, suka rasa da wanda yake.

23. Wani daga cikin almajiransa kuwa, wanda Yesu yake ƙauna, yana kishingiɗe gab da Yesu.

24. Sai Bitrus ya alamta masa ya ce, “Gaya mana, da wa yake?”

25. Shi kuwa da yake kishingiɗe haka gab da Yesu ya karkata, ya ce masa, “Ya Ubangiji, wane ne?”

26. Sai Yesu ya amsa ya ce, “Shi ne wanda zan tsoma 'yar lomar nan in ba shi.” Da ya tsoma 'yar lomar kuwa, sai ya ba Yahuza, Ɗan Saminu Iskariyoti.

27. Da karɓar 'yar loman nan Shaiɗan ya shige shi. Yesu ya ce masa, “Yi abin da za ka yi, maza.”

28. Amma cikin waɗanda suke cin abinci, ba wanda ya san dalilin da ya sa Yesu ya faɗa masa haka.

29. Har waɗansu ma sun yi zaton Yesu ya ce masa ya yi musu sayayyar idi ne, ko kuwa ya ba gajiyayyu wani abu, don Yahuza ne yake riƙe da jakar kuɗinsu.

30. Shi kuwa da karɓar 'yar lomar, sai ya fita, da dare ne kuwa.

31. Bayan ya fita kuma sai Yesu ya ce, “Yanzu ne aka ɗaukaka Ɗan Mutum, aka kuma ɗaukaka Allah ta wurinsa.

32. Allah kuma zai ɗaukaka shi zuwa ga zatinsa, nan da nan kuwa zai ɗaukaka shi.

33. Ya ku 'ya'yana ƙanana, saura ɗan lokaci kaɗan ina tare da ku. Za ku neme ni, amma kamar yadda na faɗa wa Yahudawa cewa, ‘Inda za ni ba za ku iya zuwa ba,’ haka nake faɗa muku yanzu.

34. Sabon umarni nake ba ku, shi ne ku ƙaunaci juna. Kamar yadda na ƙaunace ku, haka ku ma, ku ƙaunaci juna.

35. Ta haka, kowa zai gane ku almajiraina ne, in dai kuna ƙaunar juna.”

36. Bitrus ya ce masa, “Ya Ubangiji, ina za ka?” Yesu ya amsa ya ce, “Inda za ni, ba za ka iya bina yanzu ba, amma daga baya za ka bi ni.”

37. Bitrus ya ce masa, “Ya Ubangiji, don me, ba zan iya binka a yanzu ba? Ai, zan ba da raina saboda kai.”

Yah 13