13. Duk da haka jama'ar Isra'ila ba su kori Geshuriyawa, da Ma'akatiyawa ba, amma suka yi zamansu tare da Isra'ilawa har wa yau.
14. Kabilar Lawiyawa ne kaɗai Musa bai ba ta gādo ba, gama hadayun ƙonawa na Ubangiji, Allah na Isra'ila, su ne gādonta, kamar yadda Ubangiji ya faɗa masa.
15. Musa ya riga ya ba Ra'ubainawa nasu gādo bisa ga iyalansu.
16. Nasu yankin ƙasar ya miƙa daga Arower wadda take a gefen kwarin Arnon, da birnin da yake tsakiyar kwarin, da dukan ƙasar tudu kusa da Medeba,
17. da Heshbon, da dukan biranenta da suke kan tudu, wato Dibon, da Bamot-ba'al, da Ba'al-mayon,
18. da Yahaza, da Kedemot, da Mefayat,
19. da Kiriyatayim, da Sibma, da Zeret-shahar da yake bisa tudun da yake cikin kwarin,
20. da Bet-feyor, da gangaren Fisga, da Betyeshimot.
21. Waɗannan duka su ne birane na kan tudu, da dukan masarautar Sihon, Sarkin Amoriyawa wanda ya sarauci Heshbon. Musa ya ci shi da yaƙi da shugabannin Madayana, wato Ewi, da Rekem, da Zur, da Hur, da Reba, wato sarakunan Sihon, waɗanda suka zauna a ƙasar.
22. Jama'ar Isra'ila kuma suka kashe Bal'amu matsubbaci, ɗan Beyor, da takobi.
23. Urdun kuwa ya zama iyakar yankin ƙasar jama'ar Ra'ubainu. Wannan shi ne gādon Ra'ubainawa bisa ga iyalansu, da biranensu da ƙauyukansu.
24. Musa kuma ya ba Gadawa gādo bisa ga iyalansu.
25. Yankin ƙasarsu shi ne Yazar, da dukan biranen Gileyad da rabin ƙasar Ammonawa zuwa Arower wadda take gabas da Rabba,
26. daga Heshbon zuwa Ramat-mizfe, da Betonim, daga Mahanayim zuwa karkarar Debir,
27. da a kwarin Ber-aram, da Betnimra, da Sukkot, da Zafon, da kuma ragowar mulkin Sihon, Sarkin Heshbon. Kogin Urdun ne iyakar yankin ƙasarsu har zuwa wutsiyar Tekun Kinneret, a gabashin hayin Urdun.
28. Wannan shi ne yankin ƙasar, haɗe da garuruwa, da ƙauyuka, da aka ba mutanen kabilar Gad bisa ga iyalansu.
29. Musa kuma ya ba rabin jama'ar Manassa rabon gādo bisa ga iyalansu.
30. Yankin ƙasarsu ya bi daga Mahanayim, ya haɗa dukan Bashan, da dukan mulkin Og, Sarkin Bashan, da dukan garuruwan Yayir guda sittin da suke a Bashan,
31. da rabin Gileyad, da Ashtarot, da Edirai, wato garuruwan sarki Og a Bashan. Mutanen Makir ne, ɗan Manassa, aka ba su wannan bisa ga iyalansu.