6. Gama rana tana zuwa sa'ad da maitsaro zai yi kiraA ƙasar tudu ta Ifraimu, ya ce,‘Ku tashi mu haura zuwa SihiyonaZuwa wurin Ubangiji Allahnmu.’ ”
7. Ga abin da Ubangiji ya ce,“Raira wa Yakubu waƙar farin cikida ƙarfi,Ku ta da murya saboda shugabanal'ummai,Ku yi shela, ku yi yabo, ku ce,‘Ya Ubangiji ka ceci jama'arka,Wato ringin mutanen Isra'ila,’
8. Ga shi, zan fito da su daga ƙasararewa,Zan tattaro su daga manisantanwurare na duniya,Tare da su makafi da guragu,Da mace mai goyo da mai naƙuda,Za su komo nan a babbar ƙungiya.
9. Da kuka za su komo.Da ta'aziyya zan bishe su, in komarda su,Zan sa su yi tafiya a gefen rafuffukanruwa,A kan miƙaƙƙiyar hanya, inda baza su yi tuntuɓe ba.Gama ni uba ne ga Isra'ila,Ifraimu kuwa ɗan farina ne.”
10. “Ku ji maganar Ubangiji,Ya ku al'ummai,Ku yi shelarsa har a ƙasashen da sukenesa, na gāɓar teku.Ku ce, ‘Shi wanda ya warwatsaIsra'ila zai tattaro ta,Zai kiyaye ta kamar yadda makiyayiyakan kiyaye garkensa.’
11. Gama Ubangiji ya fanshi Yakubu.Ya fanshe shi daga hannuwanwaɗanda suka fi ƙarfinsa.
12. Za su zo su raira waƙa da ƙarfi,A bisa ƙwanƙolin Sihiyona,Za su yi annuri saboda alherinUbangiji,Saboda hatsi, da ruwan inabi, damai,Saboda 'ya'yan tumaki da na shanu.Rayuwarsu za ta zama kamarlambu,Ba za su ƙara yin yaushi ba.
13. Sa'an nan 'yan mata za su yi rawada farin ciki,Samari da tsofaffi za su yi murna.Zan mai da makokinsu ya zamamurna,Zan ta'azantar da su, in ba su farinciki maimakon baƙin ciki.
14. Zan yi wa ran firistoci biki dawadata,Jama'ata za su ƙoshi da alherina,Ni Ubangiji na faɗa.”
15. Ga abin da Ubangiji ya ce,“An ji murya daga Rama,Muryar baƙin ciki da kuka mai zafi,Rahila tana kuka saboda 'ya'yanta,ba su.
16. Ki yi shiru, ki daina kuka,Ki shafe hawaye daga idanunki.Za a sāka miki wahalarki,Za su komo daga ƙasar abokin gāba,Ni Ubangiji na faɗa.
17. Akwai sa zuciya dominki a nangaba,Ni Ubangiji na faɗa.'Ya'yanki za su komo ƙasarsu.