Far 41:22-37 Littafi Mai Tsarki (HAU)

22. Har yanzu kuma, a cikin mafarkina ga zangarku masu kauri kyawawa guda bakwai, suna girma a kara guda,

23. zangarku bakwai kuma busassu sirara waɗanda iskar gabas ta ƙeƙasar, suka fito a bayansu.

24. Siraran zangarkun kuwa suka haɗiye zangarkun nan bakwai kyawawa masu kauri. Na faɗa wa bokaye, amma ba wanda ya iya yi mini fassararsa.”

25. Yusufu ya ce wa Fir'auna, “Mafarkin Fir'auna ɗaya ne, Allah ya bayyana wa Fir'auna abin da yake shirin aikatawa.

26. Waɗannan shanu bakwai, shekaru bakwai ne, kyawawan zangarkun nan bakwai kuma shekaru bakwai ne, mafarkin ɗaya ne.

27. Ramammun shanun nan bakwai da suka fito a bayansu shekaru bakwai ne, busassun zangarkun nan bakwai waɗanda iskar gabas ta ƙeƙasar kuwa, shekaru bakwai ne na yunwa.

28. Haka yake kamar yadda na faɗa wa Fir'auna, Allah ya nuna wa Fir'auna abin da yake shirin aikatawa.

29. Za a yi shekara bakwai cike da ƙoshi a ƙasar Masar duka,

30. amma a bayansu za a yi shekara bakwai na yunwa, amma za a manta da dukan ƙoshin nan a ƙasar Masar, yunwar kuwa za ta game dukan ƙasar.

31. Zai kuwa zama kamar ba a taɓa yin ƙoshi a ƙasar ba, saboda tsananin yunwar.

32. Maimaitawar mafarkin nan na Fir'auna kuwa, ya nuna cewa Allah ya riga ya ƙaddara al'amarin, hakika kuwa Allah zai tabbatar da shi ba da jimawa ba.

33. “Yanzu fa bari Fir'auna ya zaɓi mutum mai basira, mai hikima, ya sa shi bisa ƙasar Masar.

34. Bari Fir'auna ya ci gaba da naɗa shugabanni bisa ƙasa, don su tattara humushin amfanin ƙasar Masar na shekarun nan bakwai na ƙoshi.

35. Bari kuma su tattara dukan abinci a shekarun nan bakwai masu zuwa na albarka, su tsiba a ƙarƙashin ikon Fir'auna saboda abinci cikin birane, su kuma lura da shi.

36. Wannan abinci zai zama ajiya domin ƙasar, kariyar shekaru bakwai na yunwa, waɗanda za a yi cikin ƙasar Masar, domin kada ƙasar ta ƙare saboda yunwar.”

37. Fir'auna da fādawansa duka sun yarda da wannan shawara.

Far 41