1. Ikon Ubangiji kuwa ya sauko a kaina, Ruhunsa kuma ya fito da ni ya ajiye ni a tsakiyar kwari wanda yake cike da ƙasusuwa.
2. Sai ya zagaya da ni cikinsu, ga su kuwa, suna da yawa a cikin kwarin, busassu ragau.
3. Sai ya ce mini, “Ɗan mutum, waɗannan ƙasusuwa kuwa za su rayu?”Ni kuwa na amsa na ce, “Ya Ubangiji Allah, sani na gare ka.”
4. Sai ya ce mini, “Ka yi annabci a kan ƙasusuwan nan ka faɗa musu su saurari maganata.
5. Gama ni Ubangiji Allah zan hura musu numfashi, za su kuwa rayu.
6. Zan sa musu jijiyoyi da tsoka, in rufe da fata, in kuma hura musu numfashi, sa'an nan za su rayu, su sani ni ne Ubangiji.”
7. Sai na yi annabci kamar yadda ya umarce ni. Da na yi annabcin sai aka ji motsi da girgiza. Sai ƙasusuwan suka harhaɗu da juna, ƙashi ya haɗu da ƙashi a mahaɗinsu.
8. Da na duba, sai ga jijiyoyi a kansu, nama kuma ya baibaye su, sa'an nan fata ta rufe su, amma ba numfashi a cikinsu.
9. Sa'an nan Ubangiji ya ce mini, “Ɗan mutum, ka yi annabci a kan iska, ka ce mata, ni Ubangiji Allah na ce ta zo daga kusurwa huɗu, ta hura a kan waɗannan matattu domin su rayu.”
10. Na kuwa yi annabci kamar yadda aka umarce ni, sai numfashi ya shiga cikinsu, suka rayu, suka tashi, suka tsaya da ƙafafunsu. Sun zama babbar runduna ƙwarai.
11. Sa'an nan Ubangiji ya ce mini, “Ɗan mutum waɗannan ƙasusuwa su ne mutanen Isra'ila duka. Ga shi, suna cewa, ‘Ƙasusuwa sun bushe, zuciyarmu kuwa ta karai, an share mu ƙaƙaf.’
12. “Domin haka ka yi annabci ka ce musu, ni Ubangiji Allah na ce zan buɗe kaburburansu, in tashe su daga cikin kaburburansu. Zan kuma komar da su gida zuwa ƙasar Isra'ila.
13. Mutanena za su sani ni ne Ubangiji sa'ad da na buɗe kaburburansu na tashe su daga cikinsu.
14. Zan sa Ruhuna a cikinsu za su kuwa rayu. Zan sa su a ƙasarsu sa'an nan za su sani ni Ubangiji na faɗa, na kuwa aikata.”
15. Ubangiji ya kuma yi magana da ni, ya ce,
16. “Ɗan mutum, ka ɗauki sanda, ka rubuta a kansa, ‘Domin Yahuza da magoyan bayansa.’ Ka kuma ɗauki wani sanda, ka rubuta a kansa, ‘Domin Yusufu, sandan Ifraimu, da dukan mutanen Isra'ila, magoyan bayansa.’