2 Sar 5:8-20 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Amma sa'ad da Elisha, annabin Allah, ya ji cewa Sarkin Isra'ila ya keta tufafinsa, sai ya aika wa sarki ya ce, “Me ya sa ka keta tufafinka? Bari ya zo wurina, zai sani akwai annabi a Isra'ila.”

9. Na'aman kuwa da dawakansa da karusansa suka tafi suka tsaya a ƙofar gidan Elisha.

10. Sai Elisha ya aiki manzo ya faɗa wa Na'aman ya tafi, ya yi wanka a Kogin Urdun har sau bakwai, naman jikinsa zai warke, zai tsarkaka.

11. Amma Na'aman ya husata, ya yi tafiyarsa, yana cewa, “Na yi tsammani zai fito ya zo wurina ne, ya tsaya, ya yi kira sunan Ubangiji Allahnsa ya kaɗa hannunsa a wurin kuturtar, ya warkar da ni.

12. Ashe, kogin Abana da na Farfar, wato kogunan Dimashƙu, ba su fi dukan ruwayen Isra'ila ba? Da ban yi wanka a cikinsu na tsarkaka ba?” Ya juya, ya yi tafiyarsa da fushi.

13. Amma barorinsa suka je wurinsa, suka ce masa, “Ranka ya daɗe, da a ce annabin ya umarce ka ka yi wani babban abu ne, ashe, da ba ka yi ba, balle wannan, da ya ce ka tafi ka yi wanka, ka tsarkaka?”

14. Sai ya tafi ya yi wanka har sau bakwai a Kogin Urdun bisa ga maganar annabin Allah, sai naman jikinsa ya warke ya zama kamar na ƙaramin yaro, ya tsarkaka.

15. Ya kuwa komo wurin annabi Elisha shi da jama'arsa duka, ya zo ya tsaya a gabansa, ya ce, “Yanzu na sani a duniya duka ba wani Allah banda na Isra'ila, saboda haka, sai ka karɓi kyauta daga wurina.”

16. Amma Elisha ya ce, “Na rantse da Ubangiji, wanda nake bauta masa, ba zan karɓi kome ba.”Ya yi ta roƙonsa ya karɓa, amma ya ƙi.

17. Na'aman kuwa ya ce, “Da yake ka ƙi ka karɓa, ina roƙonka, ka ba baranka labtun alfadari biyu na ƙasa, gama nan gaba baranka ba zai ƙara miƙa hadaya ta ƙonawa ko baiko ga wani gunki ba, sai dai Ubangiji.

18. Sai dai Ubangiji ya gafarta mini lokacin da na bi sarki zuwa cikin haikalin Rimmon, gunkin Suriya, don ya yi sujada. Na gaskata Ubangiji zai gafarta mini.”

19. Elisha kuwa ya ce masa, “Ka sauka lafiya.” Na'aman ya tafi.Amma tun Na'aman bai yi nisa ba,

20. sai Gehazi, baran annabi Elisha, ya ce, “Duba, maigidana ya bar Na'aman Basuriyen nan ya tafi, bai karɓi kome daga cikin abin da ya kawo masa ba. Na rantse da Ubangiji, zan sheƙa a guje, in bi shi, in karɓi wani abu daga gare shi.”

2 Sar 5