2 Sam 17:11-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. Shawarata ita ce a tattara maka dukan Isra'ilawa tun daga Dan har zuwa Biyer-sheba, yawansu kamar yashi a bakin teku. Kai kuma da kanka ka tafi wurin yaƙin.

12. Da haka za mu tafi mu neme shi duk inda yake, mu fāɗa masa kamar yadda raɓa takan fāɗo bisa ƙasa. Da shi da mutanensa, ba wanda za a bari da rai.

13. Idan ya gudu zuwa cikin gari, sai dukan jama'armu su zarge garin da igiya, su jā har duk ya watse, yadda ba za a bar wani dutse a kan wani ba.”

14. Sai Absalom da dukan mutanen Isra'ila suka ce, “Shawarar Hushai Ba'arkite ta fi ta Ahitofel kyau.” Haka Ubangiji ya nufa ya wofintar da kyakkyawar shawarar Ahitofel don ya jawo wa Absalom masifa.

15. Sa'an nan Hushai ya ce wa Zadok da Abiyata, firistoci, “Ga irin shawarar da Ahitofel ya ba Absalom da dattawan Isra'ila, ga kuma irin wadda ni na bayar.

16. Yanzu sai ka aika da sauri a faɗa wa Dawuda, kada ya kwana a bakin jeji a daren yau, amma ya haye don kada a hallaka shi tare da mutanensa.”

17. Jonatan da Ahimawaz suna jira a En-rogel. Wata baranya takan tafi ta faɗa musu saƙo, su kuma sai su tafi su faɗa wa sarki Dawuda, don kada a gan su suna shiga birnin.

18. Amma wani saurayi ya gan su, sai ya faɗa wa Absalom. Sai su biyu ɗin suka gudu nan da nan. Suka shiga gidan wani mutum a Bahurim, akwai rijiya a filin gidan. Sai suka shiga rijiyar.

19. Matar gidan kuwa ta yi shimfiɗa a bakin rijiyar, ta baza tsaba a kai, ba kuwa wanda ya san abin da ta yi.

20. Sa'ad da fādawan Absalom suka zo gidan, suka tambayi matar, “Ina Ahimawaz da Jonatan suke?”Sai ta ce musu, “Ai, tuni sun haye kogi.”Sa'ad da suka neme su ba su same su ba, sai suka koma Urushalima.

21. Bayan da fādawan sun tafi, sai mutanen suka fito daga rijiyar. Suka tafi suka ce wa sarki Dawuda, “Ka tashi ka haye kogin nan da nan, gama ka ji irin muguwar shawarar da Ahitofel ya bayar a kanka.”

22. Sai Dawuda da dukan mutanen da suke tare da shi suka haye Urdun. Kafin wayewar gari ko wannensu ya haye Urdun.

2 Sam 17