2 Sam 10:13-19 Littafi Mai Tsarki (HAU)

13. Sa'an nan Yowab da mutanensa suka matsa, su gabza da Suriyawa. Suriyawa kuwa suka gudu.

14. Da Ammonawa suka ga Suriyawa sun gudu, su ma suka gudu daga gaban Abishai suka shiga birnin. Sa'an nan Yowab ya komo Urushalima daga wurin yaƙi da Ammonawa.

15. Sa'ad da Suriyawa suka ga Isra'ilawa sun ci su, suka tattara kansu.

16. Hadadezer ya aika aka kawo Suriyawan da suke a hayin Kogin Yufiretis. Suka taru a Helam. Shobak shugaban rundunar Hadadezer shi ne ya shugabance su.

17. Sa'ad da Dawuda ya ji labari, ya tara Isra'ilawa duka, ya haye Urdun zuwa Helam. Suriyawa kuwa suka ja dāgar yaƙi, suka yi yaƙi da Dawuda.

18. Amma Suriyawa suka gudu daga gaban Isra'ilawa. Dawuda kuwa ya kashe Suriyawa, mahayan karusai ɗari bakwai, da mahayan dawakai dubu arba'in (40,000). Aka yi wa Shobak shugaban rundunarsu rauni wanda ya zama ajalinsa, a can ya rasu.

19. Sa'ad da dukan hakiman Hadadezer suka ga Isra'ilawa sun ci su, sai suka yi sulhu da Isra'ilawa. Suka zama talakawansu. Wannan ya sa Suriyawa suka ji tsoron ƙara kai wa Ammonawa gudunmawa.

2 Sam 10