5. Gama Sulemanu ya bi Ashtoret ta Sidoniyawa, da Milkom, wato gunkin Ammonawa.
6. Ya yi wa Ubangiji zunubi. Bai bi Ubangiji da zuciya ɗaya kamar yadda tsohonsa, Dawuda, ya yi ba.
7. Sulemanu ya gina wa Kemosh, wato gunkin Mowab, da Molek, gunkin Ammonawa, masujadai a kan dutsen da yake gabas da Urushalima.
8. Ya kuma gina masujadai inda dukan matansa baƙi za su riƙa miƙa turare da hadayu ga gumakansu.
9. Ubangiji kuwa ya yi fushi da Sulemanu, domin zuciyar Sulemanu ta rabu da Ubangiji, Allah na Isra'ila, wanda ya bayyana a gare shi sau biyu,
10. ya kuma umarce shi kada ya bi gumaka. Amma bai kiyaye umarnin da Ubangiji ya yi masa ba.
11. Saboda haka Ubangiji ya ce wa Sulemanu, “Tun da yake ka yi haka, ba ka kuwa kiyaye umarnina da dokokina waɗanda na umarce ka da su ba, to, hakika zan ƙwace mulki daga gare ka, in ba baranka.
12. Amma saboda tsohonka, Dawuda, ba zan ƙwace a zamaninka ba, amma zan ƙwace daga hannun ɗanka.
13. Duk da haka ba zan ƙwace mulkin duka ba, amma zan ba ɗanka kabila guda, saboda bawana Dawuda, saboda kuma Urushalima wadda na zaɓa.”
14. Ubangiji kuwa ya sa Hadad Ba'edome, ya tayar wa Sulemanu. Shi Hadad daga jinin sarautar Edom ne.
15. Gama sa'ad da Dawuda ya ci Edom, Yowab, shugaban sojoji, ya tafi don ya binne kisassu, sun yi wata shida a can, shi da mutanensa, sai ya kashe kowane namijin da yake cikin Edom.
16. Gama Yowab da dukan Isra'ilawa sun tsaya a Edom wata shida, sai da ya gama kashe mazajen Edom duka.
17. Amma Hadad ya tsere zuwa Masar tare da waɗansu Edomawa, barorin tsohonsa. Hadad yana ɗan saurayi a lokacin.
18. Suka kama hanya daga Madayana suka zo Faran. Daga Faran suka kwashi mutane tare da su, suka tafi Masar zuwa wurin Fir'auna, Sarkin Masar, wanda ya ba shi gida, ya kuma riƙa ba shi abinci, ya kuma ba shi ƙasa.
19. Hadad kuwa ya sami farin jini ƙwarai a wurin Fir'auna, har ya aurar masa da ƙanwar matarsa, wato ƙanwar Tafenes, sarauniya.
20. Ita kuwa ta haifa masa ɗa, Genubat, wanda Tafenes ta yi renonsa a gidan Fir'auna. Genubat kuwa ya zauna tare da 'ya'yan Fir'auna, maza.
21. Amma sa'ad da Hadad ya ji labari Dawuda ya rasu, Yowab shugaban sojoji shi ma ya rasu, sai Hadad ya ce wa Fir'auna, “Ka yardar mini, in tashi, in koma ƙasata.”
22. Amma Fir'auna ya ce masa, “Me ka rasa a nan har da kake so ka koma ƙasarka?”Hadad ya ce masa, “Ka dai yardar mini kawai in tafi.” Ya kuwa koma ƙasarsa.