1 Sam 28:13-25 Littafi Mai Tsarki (HAU)

13. Sarki kuwa ya ce mata, “Kada ki ji tsoro, me kike gani?”Ta ce masa, “Na ga wani allah yana fitowa daga ƙasa.”

14. Ya ce mata, “Yaya kamanninsa yake?”Ta ce, “Wani tsoho ne yake hawowa, yana naɗe da alkyabba.”Saul ya gane Sama'ila ne, sai ya sunkuyar da kai, ya durƙusa har ƙasa da bangirma.

15. Sai Sama'ila ya ce wa Saul, “Don me ka dame ni, ka hawar da ni?”Saul ya ce, “Ina cikin babbar wahala, gama Filistiyawa suna yaƙi da ni, Allah kuma ya rabu da ni, ya ƙi amsa mini ko ta wurin annabawa ko ta mafarkai, saboda haka na kira ka, ka faɗa mini abin da zan yi.”

16. Sai Sama'ila ya ce masa, “Don me za ka tambaye ni, tun da yake Ubangiji ya rabu da kai, ya zama magabcinka?

17. Ai, abin da Ubangiji ya faɗa mini a kanka, shi ne ya cika, gama Ubangiji ya fizge mulki daga hannunka, ya ba maƙwabcinka Dawuda.

18. Domin ba ka bi maganar Ubangiji ba, ba ka zartar da hukuncinsa mai zafi a kan Amalekawa ba, saboda haka Ubangiji ya yi maka haka yau.

19. Banda haka kuma Ubangiji zai ba da Isra'ilawa tare da kai a hannun Filistiyawa. Gobe, da kai da 'ya'yanka maza za ku kasance tare da ni. Ubangiji zai ba da rundunar yaƙin Isra'ila a hannun Filistiyawa.”

20. Da jin maganar Sama'ila sai Saul ya faɗi ƙasa warwar. Tsoro ya kama shi ƙwarai. Ba shi kuma da ƙarfi domin bai ci kome dukan yini da dukan dare ba.

21. Sai matar ta zo wurin Saul, da ta ga ya tsorata, sai ta ce masa, “Baiwarka ta yi kasai da ranta, ta kuwa kasa kunne gare ka.

22. To, kai ma ka kasa kunne ga baiwarka. Bari in ba ka abinci, ka ci don ka sami ƙarfin tafiya.”

23. Sai ya ƙi, ya ce, “Ba zan ci abinci ba.” Sai da barorinsa da matar suka roƙe shi, sa'an nan ya ji maganarsu, ya tashi daga ƙasa, ya zauna a bakin gado.

24. Matar kuwa ta yi hanzari ta yanka turkakken maraƙinta, ta ɗauki gari ta kwaɓa, ta toya abinci marar yisti da shi.

25. Sa'an nan ta kawo wa Saul da barorinsa, suka ci, sa'an nan suka tashi suka tafi da daren nan.

1 Sam 28