2. Sama'ila kuwa ya ce, “Ƙaƙa zan yi wannan? Gama idan Saul ya ji zai kashe ni.”Sai Ubangiji ya ce, “Ka tafi da ɗan maraƙi, ka ce, ka zo ne ka miƙa wa Ubangiji hadaya.
3. Ka gayyaci Yesse zuwa wurin hadayar, zan nuna maka abin da za ka yi. Za ka zuba wa wanda na nuna maka mai.”
4. Sama'ila ya yi yadda Ubangiji ya faɗa masa, ya tafi Baitalami, inda dattawan garin suka tarye shi da rawar jiki, suka ce masa, “Maigani, wannan ziyara lafiya kuwa?”
5. Ya ce, “I, lafiya lau. Na zo ne in miƙa wa Ubangiji hadaya, sai ku tsarkake kanku, ku zo mu tafi wurin yin hadaya tare.” Ya kuma sa Yesse da 'ya'yansa maza su tsarkake kansu, su je wurin hadayar.
6. Da suka isa wurin hadayar, Sama'ila ya ga Eliyab, ɗan Yesse, sai ya zaci shi ne wanda Ubangiji ya zaɓa.
7. Amma Ubangiji ya ce masa, “Kada ka kula da kyan tsarinsa, ko tsayinsa, domin ba shi nake so ba, gama yadda Ubangiji yake gani, ba haka mutum yake gani ba. Mutum yakan dubi kyan tsari ne kawai, amma Ubangiji yakan dubi zuciya.”
8. Sa'an nan Yesse ya kira Abinadab ya wuce a gaban Sama'ila. Amma Sama'ila ya ce, “Ubangiji kuma bai zaɓi wannan ba.”
9. Sa'an nan Yesse ya sa Shimeya ya zo. Sama'ila kuma ya ce, “Ubangiji bai zaɓi wannan ba.”
10. Ta haka Yesse ya sa 'ya'yansa maza, su bakwai, suka zo a gaban Sama'ila. Sama'ila kuwa ya ce wa Yesse, “Ubangiji bai zaɓi waɗannan ba.”
11. Sai ya tambayi Yesse, “Ko kana da sauran waɗansu 'ya'ya maza?”Yesse ya ce, “Da sauran autan, ga shi kuma, yana wurin kiwon tumaki.”Sama'ila ya ce masa, “Sai ka aika a taho da shi, gama ba zan koma ba, sai ya zo.”
12. Yesse kuwa ya aika aka taho da shi. Ga shi kuwa kyakkyawa ne, idanunsa suna sheƙi. Sai Ubangiji ya ce wa Sama'ila, “Tashi ka zuba masa man keɓewa, shi ne sarkin.”
13. Sama'ila ya ɗauki man zaitun, ya zuba masa a gaban 'yan'uwansa. Ruhun Ubangiji ya sauko da iko a kan Dawuda tun daga wannan rana zuwa gaba. Sama'ila kuwa ya tashi, ya koma Rama.
14. Yanzu kuwa Ruhun Ubangiji ya rabu da Saul, sai Ubangiji ya sa mugun ruhu ya azabtar da shi.