10. Ba kome a gonaki,Ƙasa tana makoki,Domin an lalatar da hatsin,'Ya'yan inabi sun bushe,Itatuwan zaitun kuma sun yi yaushi.
11. Ya ku manoma, ku yi baƙin ciki,Ku yi kuka, ku da kuke lura dagonakin inabi,Gama alkama, da sha'ir,Da dukan amfanin gonaki sunlalace.
12. Kurangar inabi ta bushe,Itatuwan ɓaure kuma sun yi yaushi,Rumman, da dabino, da gawasa,Da dukan itatuwan gonaki sunbushe.Murna ta ƙare a wurin mutane.
13. Ya ku firistoci masu miƙa hadayu abagaden Ubangiji,Ku sa tufafin makoki, ku yi kuka!Ku shiga Haikali, ku kwana,Kuna saye da tufafin makoki,Gama ba hatsi ko ruwan inabi da zaa yi hadaya da su,A cikin Haikalin Allahnku.
14. Ku sa a yi azumi,Ku kira muhimmin taro.Ku tara dattawa da dukan mutanenƙasarA Haikalin Ubangiji Allahnku,Ku yi kuka ga Ubangiji.
15. Taku ta ƙare a wannan rana!Gama ranar Ubangiji ta kusa,Halaka daga wurin Maɗaukaki ta zo.
16. An lalatar da amfanin gonaki a kanidonmu,Ba murna a Haikalin Allahnmu.
17. Itatuwa sun mutu a busasshiyarƙasa,Ba hatsin da za a adana a rumbu,Rumbuna sun lalace domin ba hatsi.