Yow 1:1-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Maganar Ubangiji zuwa ga Yowel, ɗan Fetuwel.

2. Ku dattawa, ku kasa kunne,Bari kowa da kowa da yake cikinYahuza, ya kasa kunne.Wani abu mai kamar wannan ya taɓafaruwa a lokacinku,Ko a lokacin kakanninku?

3. Ku faɗa wa 'ya'yanku labarinsa,'Ya'yanku kuma su faɗa wa'ya'yansu,'Ya'yansu kuma su faɗa wa tsaramai zuwa.

4. Abin da ɗango ya bari fara ta ci,Abin da fara ta bari burduduwa taci.

5. Ku farka, ku yi ta kuka, kubugaggu,Ku yi kuka, ku mashayan ruwaninabi,An lalatar da 'ya'yan inabinDa ake yin sabon ruwan inabi da su.

6. Rundunar ta aukar wa ƙasarmu,Tana da ƙarfi, ba ta kumaƙidayuwa,Haƙoranta suna da kaifi kamar nazaki.

7. Ta lalatar da kurangar inabinmu,Ta cinye itatuwan ɓaurenmu.Ta gaigaye ɓawo duka,Saboda haka rassan sun zama farifat.

8. Ya jama'a, ku yi kukaKamar yarinyar da take makokinrasuwar saurayinta.

9. Ba hatsi ko ruwan inabinDa za a yi hadaya da su cikinHaikalin.Firistoci masu miƙa wa Ubangijihadaya suna makoki.

10. Ba kome a gonaki,Ƙasa tana makoki,Domin an lalatar da hatsin,'Ya'yan inabi sun bushe,Itatuwan zaitun kuma sun yi yaushi.

11. Ya ku manoma, ku yi baƙin ciki,Ku yi kuka, ku da kuke lura dagonakin inabi,Gama alkama, da sha'ir,Da dukan amfanin gonaki sunlalace.

12. Kurangar inabi ta bushe,Itatuwan ɓaure kuma sun yi yaushi,Rumman, da dabino, da gawasa,Da dukan itatuwan gonaki sunbushe.Murna ta ƙare a wurin mutane.

Yow 1