Yah 20:12-27 Littafi Mai Tsarki (HAU)

12. sai ta ga mala'iku biyu saye da fararen tufafi a zaune inda dā gawar Yesu take, ɗaga wajen kai, ɗaya kuwa wajen ƙafafu.

13. Suka ce mata, “Uwargida, don me kike kuka?” Ta ce musu, “Ai, an ɗauke Ubangijina, ban kuwa san inda aka sa shi ba.”

14. Da ta faɗi haka sai ta juya ta ga Yesu tsaye, amma ba ta gane Yesu ne ba.

15. Yesu ya ce mata, “Uwargida, don me kike kuka? Wa kuma kike nema?” Saboda kuma ta zaci shi ne mai aikin lambun, ta ce masa, “Maigida, in kai ne ka ɗauke shi, gaya mini inda ka sa shi mana, ni kuwa in ɗauke shi.”

16. Yesu ya ce mata, “Maryamu!” Sai ta juya ta ce masa da Yahudanci, “Rabboni!” wato Malam.

17. Yesu ya ce mata, “Kada ki riƙe ni, domin har yanzu ban hau wurin Uba ba tukuna. Sai dai ki tafi wurin 'yan'uwana ki ce musu ina hawa wurin Ubana kuma Ubanku, Allahna kuma Allahnku.”

18. Sai Maryamu Magadaliya ta je ta ce wa almajiran, “Na ga Ubangiji!” Ta kuma ce shi ya faɗa mata waɗannan abubuwa.

19. A ran nan da magariba, ranar farko ta mako, ƙofofin ɗakin da almajiran suke ciki na kulle don tsoron Yahudawa, sai ga Yesu ya zo ya tsaya a tsaka, ya ce musu, “Salama alaikun!”

20. Da ya faɗi haka, ya nuna musu hannuwansa da kwiɓinsa. Sai almajiran suka yi farin ciki da ganin Ubangiji.

21. Sai Yesu ya sāke ce musu, “Salama alaikun! Kamar yadda Uba ya aiko ni, haka ni ma na aike ku.”

22. Da ya faɗi haka ya busa musu numfashinsa, ya ce musu, “Ku karɓi Ruhu Mai Tsarki.

23. Duk waɗanda kuka gafarta wa zunubansu, an gafarta musu ke nan. Duk waɗanda ba ku gafarta wa ba kuwa, ba a gafarta ba ke nan.”

24. Toma kuwa, ɗaya daga cikin goma sha biyun nan, wanda ake kira Ɗan Tagwai, ba ya nan tare da su sa'ad da Yesu ya zo.

25. Sai sauran almajiran suka ce masa, “Mun ga Ubangiji.” Amma ya ce musu, “In ban ga gurbin ƙusoshi a hannuwansa ba, in sa yatsata a gurbin ƙusoshin, in kuma sa hannuna a kwiɓinsa ba, ba zan ba da gaskiya ba.”

26. Bayan kwana takwas har wa yau almajiransa na cikin gidan, Toma ma yana nan tare da su, ƙofofi suna kulle, sai ga Yesu ya zo ya tsaya a tsaka, ya ce, “Salama alaikun.”

27. Sa'an nan ya ce wa Toma, “Sa yatsanka nan, ka ji hannuwana. Miƙo hannunka kuma ka sa a kwiɓina. Kada ka zama marar ba da gaskiya, sai dai mai ba da gaskiya.”

Yah 20