11. Wannan ce mu'ujizar farko da Yesu ya yi, ya kuwa yi ta ne a Kana ta ƙasar Galili, ya bayyana ɗaukakarsa. Almajiransa kuma suka gaskata da shi.
12. Bayan haka sai ya tafi Kafarnahum, da shi da uwa tasa, da 'yan'uwansa, da kuma almajiransa, suka zauna a can 'yan kwanaki.
13. Idin Ƙetarewa na Yahudawa ya matso, sai Yesu ya tafi Urushalima.
14. A cikin Haikali ya sami waɗansu dillalan shanu, da na tumaki, da na tattabarai, da kuma 'yan canjin kuɗi zaune wurin aikinsu.
15. Sai ya tuka bulala mai harsuna ta igiya, ya kore su duka daga Haikalin, har da tumakin da shanun, ya kuma watsar da kuɗin 'yan canjin, ya birkice teburorinsu.
16. Ya ce da dillalan tattabarai, “Ku kwashe waɗannan daga nan, kada ku mai da Haikalin Ubana kasuwa.”
17. Sai almajiransa suka tuna a rubuce yake cewa, “Kishin Haikalinka ya ci raina matuƙa.”
18. Sai Yahudawa suka amsa masa suka ce, “Wace mu'ujiza za ka nuna mana da kake haka?”
19. Yesu ya amsa musu ya ce, “Ku rushe Haikalin nan, ni kuwa in ta da shi a cikin kwana uku.”
20. Yahudawa suka ce, “Sai fa da aka shekara arba'in da shida ana ginin Haikalin nan, kai kuwa a cikin kwana uku za ka ta da shi?”
21. Amma haikalin da Yesu ya ambata jikinsa ne.
22. Saboda haka bayan an tashe shi daga matattu, almajiransa suka tuna ya faɗi haka, suka kuma gaskata Nassi da maganar da Yesu ya faɗa.