43. Lawiyawan da suka komo daga zaman talala, Yeshuwa da Kadmiyel na zuriyar Hodawiya, saba'in da huɗu.
44. Mawaƙa, na zuriyar Asaf, ɗari da arba'in da takwas.
45. Masu tsaron Haikali su ne zuriyar Shallum, da Ater, da Talmon, da Akkub, da Hatita, da Shobai, ɗari da talatin da takwas.
60. Jimillar zuriyar ma'aikatan Haikali da na Sulemanu, su ɗari uku da tasa'in da biyu ne.
63. Na wajen firistoci kuma su ne zuriyar Habaya, da na Hakkoz, da na Barzillai, wanda ya auri 'yar Barzillai mutumin Gileyad, aka kira shi da sunan zuriyar surukinsa.
64. Waɗannan suka nema a rubuta su tare da waɗanda aka rubuta jerin sunayen asalinsu, amma ba a same su a ciki ba, saboda haka aka hana su shiga cikin firistoci, sun zama kamar marasa tsarki.
65. Sai mai mulki ya faɗa musu kada su ci abinci mafi tsarki, sai an sami firist wanda zai yi tambaya ta wurin Urim da Tummin tukuna.