Neh 12:25-30 Littafi Mai Tsarki (HAU)

25. Mattaniya, da Bakbukiya, da Obadiya, da Meshullam, da Talmon, da Akkub su ne masu tsaron ƙofofi, suna tsaron ɗakunan ajiya na wajen ƙofofi.

26. Waɗannan suna nan a zamanin Yoyakim ɗan Yeshuwa, jikan Yehozadak, da zamanin mai mulki Nehemiya, da Ezra, firist da magatakarda.

27. A lokacin keɓe garun Urushalima, sai aka nemo Lawiyawa a wurarensu duka don a kawo su Urushalima, su yi bikin keɓewa da farin ciki da godiya, da raira waƙoƙi da kuge, da garaya, da molo.

28. Aka tattara mawaƙa daga kewayen Urushalima da ƙauyukan Netofatiyawa.

29. Da kuma daga Betgilgal da karkarar Geba, da Azmawet, gama mawaƙan sun gina wa kansu ƙauyuka kewaye da Urushalima.

30. Sai firistoci da Lawiyawa suka tsarkake kansu, suka kuma tsarkake jama'a, da ƙofofi, da garun.

Neh 12