Mat 16:13-28 Littafi Mai Tsarki (HAU)

13. To, da Yesu ya shiga ƙasar Kaisariya Filibi, sai ya tambayi almajiransa ya ce, “Wa mutane suke cewa, Ɗan Mutum yake?”

14. Sai suka ce, “Waɗansu suna cewa, Yahaya Maibaftisma, waɗansu kuwa Iliya, waɗansu kuma Irmiya, ko kuwa ɗaya daga cikin annabawa.”

15. Ya ce musu, “Amma ku fa, wa kuke cewa, nake?”

16. Sai Bitrus ya amsa, ya ce, “Kai ne Almasihu, Ɗan Allah Rayayye.”

17. Yesu ya amsa masa ya ce, “Kai mai albarka ne, Saminu, ɗan Yunusa! Domin ba ɗan adam ne ya bayyana maka wannan ba, sai dai Ubana da yake cikin Sama.

18. Ina dai gaya maka, kai ne Bitrus, a kan dutsen nan ne zan gina ikilisiyata, wadda ikon Hades ba zai rinjaye ta ba.

19. Zan ba ka mabuɗan Mulkin Sama. Kome ka ƙulla a duniya, zai zama abin da aka riga ƙullewa a Sama ne. Kome ka warware a duniya, zai zama abin da aka riga warwarewa a Sama ne.”

20. Sai ya kwaɓi almajiransa ƙwarai kada su gaya wa kowa shi ne Almasihu.

21. Tun daga lokacin nan Yesu ya fara bayyana wa almajiransa, lalle ne ya tafi Urushalima, ya sha wuya iri iri a hannun shugabanni da manyan firistoci da malaman Attaura, har a kashe shi, a rana ta uku kuma a tashe shi.

22. Sai Bitrus ya ja shi waje ɗaya, ya fara tsawata masa, ya ce, “Allah ya sawwaƙe, ya Ubangiji! Wannan har abada ba zai same ka ba!”

23. Amma Yesu ya juya ya ce wa Bitrus, “Ka yi nesa da ni, ya Shaiɗan! Tarko kake a gare ni. Ba ka tattalin al'amuran Allah, sai dai na mutane.”

24. Sai Yesu ya ce wa almajiransa, “Duk mai son bina, sai ya ƙi kansa, ya ɗauki gicciyensa, ya bi ni.

25. Duk mai son tattalin ransa, zai rasa shi. Duk kuwa wanda ya rasa ransa saboda ni, zai same shi.

26. Me mutum ya amfana in ya sami duniya duka a bakin ransa? Me kuma mutum zai iya bayarwa ya fanshi ransa?

27. Domin Ɗan Mutum zai zo da ɗaukakar Ubansa tare da mala'ikunsa. A sa'an nan ne zai sāka wa kowane mutum gwargwadon aikinsa.

28. Hakika, ina gaya muku, akwai waɗansu tsaitsaye a nan da ba za su mutu ba, sai sun ga Ɗan Mutum yana zuwa cikin Mulkinsa.”

Mat 16