16. Ubangiji kansa ya watsar da su,Ba zai ƙara kulawa da su ba.Ba su darajanta firistoci ba,Ba su kuma kula da dattawa ba.
17. Idanunmu sun gajiDa zuba ido a banza don samun taimako,Mun zuba idoGa al'ummar da ba za ta iya cetonmu ba.
18. Ana bin sawayenmu,Don haka ba mu iya tafiya a titunanmu ba.Ƙarshenmu ya yi kusa,Kwanakinmu sun ƙare,Gama ƙarshenmu ya zo.
19. Masu runtumarmu sun fi gaggafar da take tashi sama sauri.Sun fafare mu a kan duwatsu,Suna fakonmu a cikin jeji.
20. Shi wanda muke dogara gare shi,Wato zaɓaɓɓe na Ubangiji, ya auka cikin raminsu,Shi wanda muka ce,“A ƙarƙashin inuwarsa ne za mu zauna a cikin sauran al'umma.”
21. Ki yi farin ciki, ki yi murna, ke Edom,Wadda kike zaune cikin ƙasar Uz.Amma fa za a ba ki ƙoƙo ki sha,Ki bugu har ki yi tsiraici.
22. Ya Sihiyona, hukunci a kan muguntarki ya ƙare,Ba zai ƙara barinki a ƙasar bauta ba.Amma zai hukunta ki saboda muguntarki, ya Edom,Zai tone zunubanki.