Mak 2:7-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. Ubangiji ya wulakanta bagadensa,Ya kuma wofinta tsattsarkan Haikalinsa.Ya ba da garun fādodinta a hannun abokan gāba,Suka yi sowa a Haikalin UbangijiKamar a ranar idi.

8. Ubangiji ya yi niyyaYa mai da garun Sihiyona kufai,Ya auna ta da igiyar awo,Bai janye dantsensa daga hallaka ta ba.Ya sa kagara da garu su zozaye, su lalace tare.

9. Ƙofofinta sun nutse ƙasa,Ya lalatar, ya kakkarya ƙyamarenta,An kai sarkinta da mahukuntanta cikin al'ummai,Inda ba a bin dokokin annabawanta,Ba su kuma samun wahayi daga wurin Ubangiji.

10. Dattawan Sihiyona suna zaune a ƙasa shiru,Sun yi hurwa, suna saye da tufafin makoki.'Yan matan Urushalima kuma sun sunkuyar da kansu ƙasa.

11. Idanuna sun dushe saboda kuka,Raina yana cikin damuwa.Zuciyata ta karai saboda halakar mutanena,Gama 'yan yara da masu shan mamaSun suma a titunan birnin.

12. Suna yi wa uwayensu kuka, suna cewa,“Ina abinci da ruwan inabi?”Suna suma kamar mutanen da aka yi wa rauniA titunan birnin,Suna mutuwa a ƙirjin uwayensu.

13. Me zan ce miki?Da me zan kwatanta ki, ya Urushalima?Da me zan misalta wahalarkiDon in ta'azantar da ke, ya Sihiyona?Masifar da ta same ki tana da fāɗi kamar teku,Wa zai iya warkar da ke?

14. Annabawanki sun gano miki wahayan ƙarya,Ba su tone asirin muguntarki,Har da za a komo da ke daga bauta ba.Amma suka yi miki annabcin ƙarya na banza.

Mak 2