Mak 2:11-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. Idanuna sun dushe saboda kuka,Raina yana cikin damuwa.Zuciyata ta karai saboda halakar mutanena,Gama 'yan yara da masu shan mamaSun suma a titunan birnin.

12. Suna yi wa uwayensu kuka, suna cewa,“Ina abinci da ruwan inabi?”Suna suma kamar mutanen da aka yi wa rauniA titunan birnin,Suna mutuwa a ƙirjin uwayensu.

13. Me zan ce miki?Da me zan kwatanta ki, ya Urushalima?Da me zan misalta wahalarkiDon in ta'azantar da ke, ya Sihiyona?Masifar da ta same ki tana da fāɗi kamar teku,Wa zai iya warkar da ke?

14. Annabawanki sun gano miki wahayan ƙarya,Ba su tone asirin muguntarki,Har da za a komo da ke daga bauta ba.Amma suka yi miki annabcin ƙarya na banza.

15. Dukan masu wucewa suna yin miki tafin raini.Suna yi wa Urushalima tsāki,Suna kaɗa mata kai, suna cewa,“Ai, Urushalima ke nan,Birnin nan da ake cewa mai cikakken jamali,Wanda ya ƙayatar da dukan duniya?”

16. Maƙiyanki duka sun wage bakinsu gāba da ke,Suna tsāki, suna cizon bakinsu,Suna ihu, suna cewa, “Mun hallaka ta!Ai, wannan ita ce ranar da muke fata!Ga shi kuwa, ta zo, mun gan ta!”

17. Ubangiji ya aikata abin da ya yi niyya,Ya cika maganarsa wadda ya faɗa tun dā,Ya hallakar, ba tausayi,Ya sa maƙiyi ya yi murna a kanki,Ya ƙarfafa ƙarfin maƙiyanki.

Mak 2