24. Eliyasaf, ɗan Layel, shi ne shugaban gidan kakanninsa, Gershonawa.
25. 'Ya'yan Gershon, maza, su ne da aikin lura da alfarwa ta sujada da murfinta na ciki da na waje, da labulen ƙofar,
26. da labulen farfajiyar da yake kewaye da alfarwar, da bagade, da labulen ƙofar farfajiyar. Su za su lura da dukan aikin da ya shafi waɗannan abubuwa.
27. Iyalan Kohat su ne iyalin Amramawa, da na Izharawa, da na Hebronawa, da na Uzziyelawa. Waɗannan su ne iyalan Kohatawa.
28. Lissafin mazaje duka, tun daga mai wata ɗaya zuwa gaba, su dubu takwas ne da ɗari shida (8,600).
29. Iyalan 'ya'yan Kohat za su kafa zangonsu a kudancin alfarwar.
30. Elizafan ɗan Uzziyel shi ne shugaban gidan kakanninsa, Kohatawa.
31. Aikinsu shi ne lura da akwatin alkawari, da tebur, da alkuki, da bagadai, da kayayyakin Wuri Mai Tsarki waɗanda firistoci suke aiki da su, da labule, da dukan aikin da ya shafi waɗannan abubuwa.
32. Ele'azara, ɗan Haruna, firist, shi zai shugabanci shugabannin Lawiyawa, shi ne kuma zai lura da waɗanda suke aiki a Wuri Mai Tsarki.
33. Iyalan Merari su ne iyalin Maliyawa, da na Mushiyawa. Waɗannan su ne iyalan Merari.
34. Yawan mazajensu duka da aka ƙidaya tun daga mai wata ɗaya zuwa gaba, mutum dubu shida ne da ɗari biyu (6,200).
35. Shugaban gidan kakannin iyalan Merari kuwa shi ne Zuriyel, ɗan Abihail. Za su kafa zangonsu a arewacin alfarwar.
36. Aikin da aka danƙa wa 'ya'yan Merari shi ne lura da katakan alfarwar, da sanduna, da dirkoki, da kwasfa, da sauran abubuwa duka, da duk ayyukan da suka shafi waɗannan,
37. da kuma dirkoki na farfajiyar da ta kewaye wurin, da kwasfa da turaku da igiyoyinsu.
38. Waɗanda za su yi zango a gaban alfarwa ta sujada daga gabas, su ne Musa, da Haruna da 'ya'yansa maza, waɗanda aka danƙa musu tafiyar da aikin Wuri Mai Tsarki, da dukan aikin da za a yi wa Isra'ilawa. Banda su, duk wanda ya je kusa da wurin sai a kashe shi.
39. Dukan Lawiyawa waɗanda Musa da Haruna suka ƙidaya bisa ga iyalansu, bisa ga umarnin Ubangiji, tun daga mai wata ɗaya zuwa gaba, mazaje dubu ashirin da dubu biyu ne (22,000).