17. Sai Bal'amu ya koma wurin Balak ya same shi yana tsaye kusa da hadayarsa ta ƙonawa tare da dattawan Mowab. Balak kuwa ya ce masa, “Me Ubangiji ya faɗa?”
18. Sai Bal'amu ya faɗi jawabinsa, ya ce,“Tashi, Balak, ka ji,Ka kasa kunne gare ni, ya ɗan Ziffor.
19. Allah ba kamar mutum ba ne, da zai yi ƙarya,Ba kuwa ɗan mutum ba ne, da zai tuba.Zai cika dukan abin da ya alkawarta,Ya hurta, ya kuwa cika.
20. Ga shi, an umarce ni in sa albarka.Ya sa albarka, ba zan iya janye ta ba.
21. Bai ga mugunta ga Yakubu ba,Bai kuma ga wahala a Isra'ilawa ba.Ubangiji Allahnsu yana tare da su,Suna sowar murna domin shi sarkinsu ne.
22. Allah ne ya fisshe shi daga Masar,Ya yi yaƙi dominsu kamar kutunkun ɓauna.
23. Ba wata maitar da za ta cuci Yakubu,Ba kuwa sihirin da zai cuci Isra'ilawa.Yanzu za a ce, ‘Duba irin abin da Allah ya yi domin Yakubu, wato Isra'ilawa!’
24. Ga shi, jama'ar Isra'ila tana kama da ƙaƙƙarfan zaki,Ba zai kwanta ba sai ya cinye ganimarsa.Ya lashe jinin waɗanda ya kashe.”
25. Sai Balak ya ce wa Bal'amu, “Kada ka la'anta su, kada kuma ka sa musu albarka.”
26. Bal'amu kuwa ya amsa wa Balak, ya ce, “Ban faɗa maka ba, duk abin da Ubangiji ya faɗa, shi ne zan yi?”
27. Sai Balak ya ce wa Bal'amu, “In ka yarda ka zo in kai ka wani wuri, watakila Allah zai yarda ka la'anta mini su a can.”
28. Balak kuwa ya kai Bal'amu a ƙwanƙolin Dutsen Feyor wanda yake fuskantar hamada.