L. Kid 22:6-23 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. Ina roƙonka, ka zo yanzu, ka la'anta mini mutanen nan, gama sun fi ƙarfina, ko ya yiwu in ci su, in kore su daga ƙasar, gama na sani duk wanda ka sa wa albarka zai albarkatu,wanda kuwa ka la'anta, zai la'antu.”

7. Dattawan Mowab da na Madayana suka ɗauki kafin alkalami suka tafi wurin Bal'amu suka faɗa masa saƙon Balak.

8. Ya ce musu, “Ku kwana a nan, ni kuwa zan shaida muku abin da Ubangiji zai faɗa mini.” Sai dattawan Mowab suka zauna wurin Bal'amu.

9. Allah kuwa ya zo wurin Bal'amu ya ce masa, “Suwane ne mutanen da suke tare da kai?”

10. Sai Bal'amu ya ce wa Allah, “Ai, Balak ne ɗan Ziffor, Sarkin Mowab, ya aiko ya ce mini,

11. ‘Ga jama'a sun fito daga Masar, sun mamaye ƙasar, ka zo, ka la'anta mini su, watakila zan iya yin yaƙi da su, in kore su!’ ”

12. Allah kuwa ya ce wa Bal'amu, “Ba za ka tafi tare da su ba, ba kuwa za ka la'anta su ba, gama albarkatattu ne su.”

13. Da safe Bal'amu ya tashi, ya ce wa dattawan Balak, “Ku koma ƙasarku, gama Ubangiji bai yarda mini in tafi tare da ku ba.”

14. Domin haka dattawan Mowab suka tashi, suka koma wurin Balak, suka ce masa, “Bal'amu bai yarda ya biyo mu ba.”

15. Sai Balak ya sāke aiken dattawa da yawa masu daraja fiye da na dā.

16. Suka je wurin Bal'amu, suka ce masa, “Ga abin da Balak ɗan Ziffor ya ce, ‘Kada ka bar wani abu ya hana ka zuwa wurina,

17. gama zan ɗaukaka ka ƙwarai, kome kuwa ka faɗa mini in yi, zan yi, ka zo ka la'anta mini wannan jama'a.’ ”

18. Amma Bal'amu ya amsa ya ce wa barorin Balak, “Ko da a ce Balak zai ba ni gidansa cike da azurfa da zinariya, ba zan yi wani abu ko kaɗan saɓanin umarnin Ubangiji Allahna ba.

19. Amma ina roƙonku ku kwana a nan yau har in san abin da Ubangiji zai faɗa mini.”

20. Sal Allah ya je wurin Bal'amu da dare, ya ce masa, “Idan mutanen nan sun zo kiranka ne, sai ka tashi, ka tafi tare da su, amma abin da na umarce ka kaɗai za ka yi.”

21. Da safe sai Bal'amu ya tashi ya yi wa jakarsa shimfiɗa, ya tafi tare da dattawan Mowab.

22. Allah kuwa ya husata don ya tafi, mala'ikan Ubangiji ya tsaya a hanya ya tarye shi. Shi kuwa yana tafe a bisa jakarsa tare da barorinsa biyu.

23. Da jakar ta ga mala'ikan Ubangiji yana tsaye kan hanya da takobi zare a hannunsa, sai ta kauce daga hanya, ta shiga saura. Bal'amu kuwa ya buge ta don ya komar da ita a hanyar.

L. Kid 22