3. Ubangiji kuwa ya ji wa'adin Isra'ilawa, ya kuwa ba su Kan'aniyawa, suka hallaka su da biranensu ƙaƙaf. Don haka aka sa wa wurin suna Horma, wato hallakarwa.
4. Isra'ilawa suka kama hanya daga Dutsen Hor zuwa Bahar Maliya don su kauce wa ƙasar Edom. Sai jama'a suka ƙosa da hanyar.
5. Suka yi wa Allah gunaguni, da Musa kuma, suka ce, “Me ya sa kuka fitar da mu daga Masar, kuka kawo mu cikin jeji mu mutu? Gama ba abinci, ba ruwa, mu kuwa mun gundura da wannan abinci marar amfani.”
6. Sai Ubangiji ya aiko macizai masu zafin dafi a cikin jama'a, suka sassari Isra'ilawa, da yawa kuwa suka mutu.
7. Jama'a kuwa suka zo wurin Musa, suka ce, “Mun yi zunubi gama mun yi wa Ubangiji gunaguni, mun kuma yi maka. Ka roƙi Ubangiji ya kawar mana da macizan.” Musa kuwa ya yi roƙo domin jama'ar.
8. Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka ƙera maciji da tagulla, ka sarƙafa shi a bisa dirka, duk wanda maciji ya sare shi, idan ya dubi maciji na tagullar, zai rayu.”
9. Musa kuwa ya yi maciji na tagulla, ya sarƙafa shi a bisa dirka, idan kuwa maciji ya sari mutum, in ya dubi macijin tagullar, zai warke.
10. Sai mutanen Isra'ila suka kama hanya, suka yi zango a Obot.
11. Suka kama hanya daga Obot, suka yi zango a kufafen Abarim a cikin jeji daura da Mowab wajen gabas.
12. Daga can suka tashi suka sauka a Kwarin Zered.
13. Daga can kuma suka tashi suka sauka hayin Kogin Arnon, wanda yake cikin jeji wanda ya nausa zuwa iyakar Amoriyawa. Gama Arnon shi ne kan iyakar Mowabawa da Amoriyawa.
14. Saboda haka aka faɗa a Littafin Yaƙoƙi na Ubangiji cewa, “Waheb ta cikin yankin Sufa, da kwaruruka na Kogin Arnon,
15. da gangaren kwaruruka, wanda ya nausa zuwa garin Ar, ya kuma dangana da kan iyakar Mowab.”
16. Daga can suka ci gaba da tafiya zuwa Biyer, wato rijiya wadda Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka tattara mutane wuri ɗaya, zan kuwa ba su ruwa.”
17. Sai Isra'ilawa suka raira waƙa, suka ce,“Rijiya, ki ɓuɓɓugo da ruwaMu kuwa za mu raira waƙa mu gaishe ta!
18. Rijiyar da hakimai suka haƙa,Shugabannin jama'a suka haƙa,Da sandan sarauta,Da kuma sandunansu.”Daga cikin jejin suka tafi har zuwa Mattana.
19. Daga Mattana suka tafi Nahaliyel suka tafi Bamot.