7. Sai firist ɗin ya wanke tufafinsa, ya yi wanka da ruwa, sa'an nan ya shiga zangon. Firist ɗin zai ƙazantu har zuwa maraice.
8. Shi kuma wanda ya ƙone karsanar, sai ya wanke tufafinsa, ya yi wanka da ruwa, shi ma zai ƙazantu har zuwa maraice.
9. Mutumin da yake da tsarki shi zai tara tokar karsanar, ya ajiye a wuri mai tsabta a bayan zangon. Za a adana tokar domin jama'ar Isra'ila, za a riƙa zubawa a ruwa don tsarkakewar zunubi.
10. Shi kuma wanda ya tara tokar karsanar, sai ya wanke tufafinsa zai ƙazantu har maraice. Wannan ka'ida ce ta har abada ga Isra'ilawa da baƙin da yake zama tare da su.”
11. “Duk wanda ya taɓa gawa zai ƙazantu har kwana bakwai.
12. A rana ta uku da ta bakwai zai tsarkake kansa da ruwa, zai kuwa tsarkaka, amma in a rana ta uku da ta bakwai bai tsarkake kansa ba, to, ba zai tsarkaka ba.
13. Duk wanda ya taɓa gawa, bai kuwa tsarkake kansa ba, ya ƙazantar da alfarwa ta sujada ta Ubangiji, ba za a lasafta shi cikin mutanen Allah ba, domin ba a yayyafa masa ruwan tsarkakewa ba.
14. “Wannan ita ce ka'ida a kan wanda ya rasu a alfarwa, duk wanda ya shiga alfarwar, da duk wanda yake cikin alfarwar zai ƙazantu har kwana bakwai.
15. Kowace buɗaɗɗiyarsa kuma wadda ba a rufe ba, za ta ƙazantu.
16. Wanda duk yake cikin saura ya taɓa wanda aka kashe da tokobi, ko gawa, ko ƙashin mutum, ko kabari zai ƙazantu har kwana bakwai.
17. “Don a tsarkake ƙazantar, sai a ɗiba daga cikin tokar hadaya don zunubi a cikinsa, sa'an nan a zuba ruwa mai gudu.
18. Tsarkakakken mutum zai ɗauki ɗaɗɗoya ya tsoma a ruwan, ya yayyafa wa alfarwar, da bisa kan dukan kayayyakin da suke ciki, da a kan mutanen da suke a wurin, da kan wanda ya taɓa ƙashin, ko ya taɓa wanda aka kashe, ko ya taɓa gawa, ko kabari.
19. A kan rana ta uku da ta bakwai kuma, wanda yake da tsarki zai yayyafa wa marar tsarkin ruwa, ya tsarkake shi. Sai mutumin ya wanke tufafinsa, ya yi wanka da ruwa, da maraice kuwa zai tsarkaka.
20. “Amma mutumin da ba shi da tsarki, bai kuwa tsarkake kansa ba, ba za a lasafta shi cikin jama'ar Allah ba, tun da yake ya ƙazantar da alfarwa ta sujada ta Ubangiji, gama ba a yayyafa masa ruwan da akan yayyafa wa marasa tsarki ba.