Josh 5:6-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. Gama shekara arba'in Isra'ilawa suna ta tafiya a jeji, har dukan al'umma, har da mayaƙan da suka fito daga Masar, suka hallaka, domin ba su kula da muryar Ubangiji ba. A gare su kuwa Ubangiji ya rantse, ba zai bar su su ga ƙasar da ya rantse wa kakanninsu zai ba su ba, ƙasar da take mai yalwar abinci.

7. 'Ya'yansu ne kuwa waɗanda Ubangiji ya tā da su a maimakonsu, su ne Joshuwa ya yi wa kaciya, gama ba su da kaciya, domin a hanya ba a yi musu ba.

8. Da aka gama yi wa al'ummar duka kaciya, sai suka zauna a zango har suka warke.

9. Sai Ubangiji ya ce wa Joshuwa, “A wannan rana na kawar muku da zargin Masar.” Saboda haka, har wa yau ake kiran sunan wurin Gilgal, wato a kawar.

10. Sa'ad da Isra'ilawa suke zaune a Gilgal, sai suka yi Idin Ƙetarewa a rana ta goma sha huɗu ga watan, da maraice, a filayen Yariko.

11. A kashegarin idin, a wannan rana, sai suka ci daga cikin amfanin ƙasar, waina marar yisti da busasshiyar tsaba.

12. Kashegari bayan da suka ci amfanin ƙasar kuwa, mannar ta yanke, mutanen Isra'ila kuma ba su ƙara samunta ba. A wannan shekara suka fara cin amfanin ƙasar Kan'ana.

13. Lokacin da Joshuwa yake daura da Yariko, ya ta da idanunsa ya duba, sai ya ga mutum a tsaye a gabansa da takobinsa a zare a hannunsa. Joshuwa ya tafi wurinsa, ya ce masa, “Kana wajenmu ne, ko kuwa kana wajen abokan gābanmu?”

Josh 5