Josh 4:5-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. Ya ce musu, “Wuce gaban akwatin Ubangiji Allahnku zuwa tsakiyar Urdun, ko wannenku ya ɗauki dutse a kafaɗarsa, don kowace kabila ta Isra'ila.

6. Wannan zai zama alama a gare ku, don ya yiwu wata rana 'ya'yanku za su tambaye ku, su ce, ‘Ina ma'anar waɗannan duwatsu a gare ku?’

7. Sa'an nan za ku faɗa musu cewa, ‘Domin an yanke ruwan Urdun a gaban akwatin alkawari na Ubangiji sa'ad da ya haye Urdun.’ Waɗannan duwatsu za su zama abin tunawa ga Isra'ilawa har abada.”

8. Sai Isra'ilawa suka yi yadda Joshuwa ya umarta, suka ɗauki duwatsu goma sha biyu a tsakiyar Urdun bisa ga yawan kabilansu kamar yadda Ubangiji ya faɗa wa Joshuwa, suka haye da su zuwa inda suka sauka, a can suka ajiye su.

9. Joshuwa kuma ya kafa duwatsu goma sha biyu a tsakiyar Urdun, a wurin da firistocin da suke ɗauke da akwatin alkawari suka tsaya, duwatsun suna nan har wa yau.

10. Gama firistocin da suke ɗauke da akwatin sun tsaya a tsakiyar Urdun, har aka gama dukan abin da Ubangiji ya umarci Joshuwa ya faɗa wa jama'a, da kuma bisa ga dukan abin da Musa ya umarce shi.Mutanen kuwa suka gaggauta, suka haye.

11. Da jama'a duka suka gama hayewa, sai akwatin Ubangiji da firistocin suka wuce gaban jama'ar.

12. Mutanen Ra'ubainu, da na Gad, da rabin kabilar Manassa kuwa suka haye tare da 'yan'uwansu da shirin yaƙi kamar yadda Musa ya umarce su.

Josh 4