1. Joshuwa kuma ya tara dukan kabilan Isra'ila a Shekem, ya kuma kira dattawa, da shugabanni, da alƙalai, da jarumawan Isra'ila. Suka hallara a gaban Allah.
2. Joshuwa kuwa ya ce wa mutane duka, “Ga abin da Ubangiji Allah na Isra'ila ya ce, ‘A zamanin dā kakanninku, su Tera, mahaifin Ibrahim, da Nahor, suna zaune a hayin Yufiretis. Suka bauta wa gumaka.
3. Sai na ɗauki kakanku Ibrahim daga wancan hayin Kogi, na kawo shi ƙasar Kan'ana, na sa zuriyarsa ta yawaita. Na ba shi Ishaku.
4. Ishaku kuma na ba shi Yakubu da Isuwa. Na kuma ba Isuwa ƙasar tuddai ta Seyir, ya mallake ta, amma Yakubu da 'ya'yansa suka gangara zuwa Masar.
5. Na aiki Musa da Haruna, na aukar wa Masar da annobai ta wurin abin da na yi a cikinta daga baya kuma na fisshe ku.
6. Na kuwa fitar da kakanninku daga Masar. Da suka zo Bahar Maliya, sai Masarawa suka fafari kakanninku da karusai da mahayan dawakai har zuwa teku.
7. A sa'ad da suka yi mini kuka, na sa duhu a tsakaninsu da Masarawa, na sa teku ta shafe Masarawa. Da idonku kun ga abin da na yi wa Masar, kuka kuma zauna a jeji da daɗewa.
8. Sa'an nan na kawo ku a ƙasar Amoriyawa, waɗanda suka zauna a wancan hayin Urdun, waɗanda kuma suka yi yaƙi da ku, na kuwa ba da su gare ku, na hallaka su, kuka mallaki ƙasarsu.