Josh 10:29-41 Littafi Mai Tsarki (HAU)

29. Joshuwa ya zarce, da shi da dukan Isra'ilawa zuwa Libna, suka yi yaƙi da Libna.

30. Ubangiji ya bashe ta da sarkinta a hannun Isra'ilawa, suka kuwa buge ta da takobi, da kowane mutum da yake cikinta, ba su rage kowa cikinta ba. Suka yi wa sarkinta kamar yadda suka yi wa Sarkin Yariko.

31. Joshuwa kuma ya zarce daga Libna, da shi da Isra'ilawa duka , zuwa Lakish, suka kewaye ta da yaƙi, suka auka mata.

32. Ubangiji ya ba da Lakish a hannun Isra'ilawa suka cinye ta da yaƙi cikin kwana biyu. Suka bugi kowane mutum da yake cikinta da takobi kamar yadda suka yi wa Libna.

33. Horam, Sarkin Gezer kuwa, ya kawo wa Lakish gudunmawa, Joshuwa kuwa ya buge shi tare da mutanensa, har ba wanda ya ragu.

34. Joshuwa kuma ya zarce tare da dukan Isra'ilawa daga Lakish zuwa Eglon, suka kewaye ta da yaƙi, suka auka mata.

35. A ran nan suka cinye ta, suka buge ta da kowane mutum da yake cikinta da takobi. Ya hallakar da su a wannan rana kamar yadda ya yi wa Lakish.

36. Joshuwa kuma ya haura tare da dukan Isra'ilawa daga Eglon zuwa Hebron, suka auka mata.

37. Suka cinye ta, suka buge ta, da sarkinta, da garuruwanta, da kowane mutum da yake cikinta da takobi, har ba wanda ya ragu kamar yadda ya yi wa Eglon. Ya hallakar da ita sarai duk da kowane mutum da yake cikinta.

38. Sai Joshuwa ya juya tare da dukan Isra'ilawa zuwa Debir, ya auka mata.

39. Ya cinye ta da yaƙi, da sarkinta, da garuruwanta. Ya buge ta da kowane mutum da yake cikinta da takobi, har ba wanda ya ragu. Kamar yadda ya yi wa Hebron, da Libna da sarkinta, haka kuma ya yi wa Debir da sarkinta.

40. Haka nan kuwa Joshuwa ya cinye dukan ƙasar tuddai, da Negeb, da filayen kwaruruka, da gangare, da sarakunansu duka, ba wanda ya ragu, amma ya hallaka su duka kamar yadda Ubangiji, Allah na Isra'ila ya umarta.

41. Joshuwa kuma ya cinye su da yaƙi tun daga Kadesh-barneya har zuwa Gaza, da dukan ƙasar Goshen har zuwa Gibeyon.

Josh 10