13. Sai rana ta tsaya cik, wata kuma ya tsaya,Har al'ummar ta ɗauki fansa a kan abokan gābansu.Ai, wannan a rubuce yake a littafin Yashar. Rana dai ta tsaya a tsaka, ta yi jinkirin faɗuwa da misalin yini guda.
14. Ba a taɓa yin yini kamar wannan ba, ko kafin wannan yini, ko bayansa kuma, da Ubangiji ya saurari muryar mutum. Gama Ubangiji ya yi yaƙi domin Isra'ilawa.
15. Sa'an nan Joshuwa ya koma zango a Gilgal tare da dukan Isra'ilawa.
16. Waɗannan sarakuna biyar kuma suka gudu, suka ɓuya a cikin kogo a Makkeda.
17. Aka faɗa wa Joshuwa cewa, “An sami sarakunan nan biyar, sun ɓuya a kogo a Makkeda.”
18. Sai Joshuwa ya ce, “Ku mirgina manyan duwatsu, ku rufe bakin kogon, sa'an nan ku sa mutane su yi tsaronsu.
19. Amma kada ku tsaya a can, sai ku runtumi abokan gābanku, ku bugi na bayansu, kada ku bar su su shiga biranensu, gama Ubangiji Allahnku ya riga ya ba da su a hannunku.”
20. Joshuwa da jama'ar Isra'ila suka karkashe su da yawa ƙwarai, sauransu kuma da suka ragu suka shiga birane masu garu.