Ish 61:6-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. Amma za a sani, ku firistoci ne na Ubangiji,Za ku mori dukiyar al'ummai,Za ku yi fāriya da cewa, taku ce.

7. Kunyarku da shan wulakancinku za su ƙare.Za ku zauna a ƙasarku,Za a riɓanya dukiyarku,Za ku yi ta farin ciki har abada.

8. Ubangiji ya ce,“Ina ƙaunar aikin gaskiya,Amma ina ƙin zalunci da aikata laifi.Da aminci zan ba mutanena lada,In yi madawwamin alkawari, da su.

9. Za su yi suna a cikin al'ummai,Dukan wanda ya gan su zai sani,Su ne mutanen da na sa wa albarka.”

10. Urushalima tana murna saboda abin da Ubangiji ya yi.Tana kama da amaryar da ta sha ado a ranar aurenta.Allah ya suturce ta da ceto da nasara.

11. Ba shakka, Ubangiji zai ceci jama'arsa,Kamar yadda iri yakan tsiro ya yi girma.Dukan al'ummai kuwa za su yi yabonsa.

Ish 61