1. Urushalima, ki ƙarfafa, ki yi girma kuma!Birni mai tsarki na Allah,Ki yafa wa kanki jamali!Arna ba za su ƙara shiga ta ƙofofinki ba.
2. Ki kakkaɓe kanki, ya Urushalima!Ki tashi daga cikin ƙura,Ki hau gadon sarautarki.Ki ɓaɓɓale sarƙoƙin da suke ɗaure da ke,Ke kamammiyar jama'ar Sihiyona!
3. Ubangiji ya ce wa jama'arsa,“Ba a biya kuɗi domin a saye ku ba,Amma ga shi, kuka zama bayi.Ba za a biya kuɗin fansa domin a 'yantar da ku ba,Amma, ga shi, za a 'yantar da ku.
4. Kuka taɓa zaman baƙuntaka a Masar,Daga baya Assuriyawa suka zalunce ku ba gaira ba dalili.
5. Yanzu kuma, ga shi, yana faruwa a Babila,Kuka zama kamammu a can, ba gaira ba dalili.Su da suke mulkinku suna girmankai, suna fāriya,Suna ta nuna mini raini.
6. Amma zuwa gaba za ku saniNi ne Allah, wanda na yi magana da ku.”
7. Me ya fi wannan kyau?A ga manzo yana zuwa ta kan duwatsu,Ɗauke da albishir mai daɗi, labarin salama.Ya yi shelar nasara, ya ce wa Sihiyona,“Allahnki sarki ne!”
8. Waɗanda suke tsaron birni suna sowa,Suna sowa tare saboda murna!Za su ga komowar Ubangiji a Sihiyona da idanunsu!