13. Kuna mantawa da Ubangiji wanda ya halicce ku,Wanda ya shimfiɗa sammai,Ya kuma kafa harsashin ginin duniya?Don me za ku yi ta jin tsoron fushin waɗanda suke zaluntarku,Da waɗanda suke shiri su hallaka ku?Fushinsu ba zai taɓa yi muku kome ba!
14. 'Yan sarƙa za su fita ba da jimawa baZa su yi tsawon rai,Su kuma sami dukan abincin da suke bukata.
15. “Ni ne Ubangiji Allahnku,Na dama tekuNa sa raƙumanta suka yi ruri.Sunana Ubangiji Mai Iko Dukka!
16. Na shimfiɗa sammai,Na kafa harsashin ginin duniya,Na ce wa Sihiyona, ‘Ku jama'ata ne!Na ba ku koyarwata,Na kuwa kiyaye ku da ikona.’ ”
17. Ya Urushalima, ki farka!Ki tashi da kanki, ki miƙe!Kika sha ƙoƙon hukunci wanda Ubangiji, cikin fushinsa, ya ba ki ki sha,Kika shanye shi, ya kuwa sa ki yi tangaɗi!
18. Ba wanda zai yi miki jagora,Ba wani daga cikin mutanenkiDa zai kama hannunki.
19. Masifa riɓi biyu ta auko miki,Yaƙi ya lalatar da ƙasarki,Mutanenki suka tagayyara da yunwa.
20. A kan kusurwar kowane titiMutanenki sun rafke saboda rashin ƙarfi,Sun zama kamar barewa da tarkon maharbi ya kama.Suka ji ƙarfin fushin Allah.
21. Ku mutanen Urushalima, masu shan wahala,Ku da kuke tangaɗi kamar waɗanda suka bugu,
22. Ubangiji Allahnku ya kāre ku ya ce,“Ina ɗauke ƙoƙon da na ba ku cikin fushina.Ba za ku ƙara shan ruwan inabin da zai sa ku yi tangaɗi ba.