Ish 51:11-23 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. Su waɗanda ka fansaZa su kai Urushalima da farin ciki,Da waƙa, da sowa ta murna.Za su yi ta murna har abada,Ba sauran baƙin ciki ko ɓacin zuciya har abada.

12. Ubangiji ya ce,“Ni ne wanda yake ƙarfafa ku.Don me za ku ji tsoron mutum mai mutuwa,Wanda bai fi ciyawa tsawon rai ba?

13. Kuna mantawa da Ubangiji wanda ya halicce ku,Wanda ya shimfiɗa sammai,Ya kuma kafa harsashin ginin duniya?Don me za ku yi ta jin tsoron fushin waɗanda suke zaluntarku,Da waɗanda suke shiri su hallaka ku?Fushinsu ba zai taɓa yi muku kome ba!

14. 'Yan sarƙa za su fita ba da jimawa baZa su yi tsawon rai,Su kuma sami dukan abincin da suke bukata.

15. “Ni ne Ubangiji Allahnku,Na dama tekuNa sa raƙumanta suka yi ruri.Sunana Ubangiji Mai Iko Dukka!

16. Na shimfiɗa sammai,Na kafa harsashin ginin duniya,Na ce wa Sihiyona, ‘Ku jama'ata ne!Na ba ku koyarwata,Na kuwa kiyaye ku da ikona.’ ”

17. Ya Urushalima, ki farka!Ki tashi da kanki, ki miƙe!Kika sha ƙoƙon hukunci wanda Ubangiji, cikin fushinsa, ya ba ki ki sha,Kika shanye shi, ya kuwa sa ki yi tangaɗi!

18. Ba wanda zai yi miki jagora,Ba wani daga cikin mutanenkiDa zai kama hannunki.

19. Masifa riɓi biyu ta auko miki,Yaƙi ya lalatar da ƙasarki,Mutanenki suka tagayyara da yunwa.

20. A kan kusurwar kowane titiMutanenki sun rafke saboda rashin ƙarfi,Sun zama kamar barewa da tarkon maharbi ya kama.Suka ji ƙarfin fushin Allah.

21. Ku mutanen Urushalima, masu shan wahala,Ku da kuke tangaɗi kamar waɗanda suka bugu,

22. Ubangiji Allahnku ya kāre ku ya ce,“Ina ɗauke ƙoƙon da na ba ku cikin fushina.Ba za ku ƙara shan ruwan inabin da zai sa ku yi tangaɗi ba.

23. Zan ba da shi ga waɗanda suke zaluntarku,Su waɗanda suka sa kuka kwanta a titunaSuka tattake ku, sai ka ce kun zama ƙura.”

Ish 51