1. Ku kasa kunne gare ni, ku al'ummai manisanta,Ku mutanen da suke zaune a can nesa!Ubangiji ya zaɓe ni, tun kafin a haife ni,Ya kuwa sa ni in zama bawansa.
2. Ya sa maganata ta yi kaifi kamar takobi,Ya kiyaye ni da ikonsa.Ya sa na zama kamar kibiyaMai tsini shirayayyiya domin harbi.
3. Ya ce mini, “Isra'ila, kai bawana ne.Mutane za su yabe ni saboda kai.”
4. Na ce, “Na yi aiki, amma a banza ne.Na mori ƙarfina, amma ban ƙulla kome ba.”Duk da haka na dogara ga Ubangiji, ya daidaita al'amura,Shi zai sāka mini abin da na yi.
5. Ubangiji ya zaɓe ni tun kafin a haife ni.Ya maishe ni bawansa domin in komo da mutanensa,In komo da jama'ar Isra'ilan da aka warwatsar.Ubangiji ya ba ni daraja,Shi ne tushen ƙarfina.
6. Ubangiji ya ce mini,“Bawana, ina da aiki mai girma dominka,Ba komo da girman jama'ar Isra'ila da suka ragu kaɗai ba,Amma zan sa ka zama haske ga al'ummai,Domin dukan duniya ta tsira.”
7. Allah Mai Tsarki na Isra'ila, Mai Fansa,Ya ce wa wanda aka raina ƙwarai,Al'ummai suka ƙi shi,Bawa na masu mulki kuma,“Sarakuna za su gan ka a sake,Su kuma miƙe tsaye su ba ka girma,Shugabanni su kuma za su gani,Su rusuna har ƙasa su ba ka girma.”Wannan kuwa zai faru saboda Ubangiji,Allah Mai Tsarki na Isra'ila, ya zaɓi bawansa,Ya kuwa cika alkawaransa.