21. Tsawon kowane ginshiƙi kamu goma sha takwas ne, kewayensa kuwa kamu goma sha biyu ne, kaurinsa kuma taƙi huɗu ne. Kowannensu yana da rami a ciki.
22. A kan kowane ginshiƙi, an yi masa dajiyar tagulla, tsayinta kamu biyar. A bisa kan kowace dajiya akwai raga da siffofin rumman na tagulla kewaye da dajiyar. Ginshiƙi na biyu ma haka yake da siffofin rumman.
23. Akwai siffofin rumman tasa'in da shida da ake gani a gyaffan. Dukan siffofin rumman da suke a kan ragar kewaye, guda ɗari ne.
24. Shugaban matsara kuma ya ɗauki Seraiya babban firist, da Zafaniya wanda yake biye da babban firist, da mutum uku masu tsaron ƙofar Haikali, ya tafi da su.
25. Daga cikin birnin kuma ya ɗauki shugaban sojojin, da mutum bakwai 'yan majalisar sarki, da magatakardan shugaban sojojin wanda yakan tara sojojin ƙasar, da mutane sittin na ƙasar, waɗanda aka same su a birnin, ya tafi da su.
26. Nebuzaradan shugaban matsara ya tafi da waɗannan mutane wurin Sarkin Babila a Ribla,
27. Sarkin Babila kuwa ya kashe su a Ribla a ƙasar Hamat.Haka aka tafi da mutanen Yahuza bautar talala.
28. Wannan shi ne yawan mutanen da Nebukadnezzar ya kai su bauta. A shekara ta bakwai ta sarautarsa, ya tafi da Yahudawa dubu uku da ashirin da uku (3,023).
29. A shekara ta goma sha takwas ta sarautarsa, ya tafi da Yahudawa daga Urushalima ɗari takwas da talatin da biyu.
30. A shekara ta ashirin da uku ta sarautarsa kuma, Nebuzaradan shugaban matsara ya tafi da Yahudawa ɗari bakwai da arba'in da biyar. Jimillarsu duka kuwa dubu huɗu da ɗari shida ne (4.600).